Bayan Tsige Gwamnoni 3, Kotun Daukaka Ƙara Ta Tsaida Ranar Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan APC
- Kotun ɗaukaka ƙara ta tsaida ranar yanke hukunci kan sahihin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Nasarawa
- Gwamna Abdullahi Sule na APC ne ya ɗaukaka kara bayan kotun zaɓe ta tsige shi, ta ce ɗan takarar PDP ne zababben gwamna
- Tuni dai rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta ƙara tsaurara matakan tsaro domin tabbatar da zaman lafiya gabanin yanke hukunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a birnin tarayya Abuja ta tsaida ranar Alhamis, 23 ga watan Nuwamba, 2023 a matsayin ranar yanke hukunci a shari'ar zaɓen gwamnan jihar Nasarawa.
Kotun zata raba gardama ne tsakanin Gwamna Abdullahi Sule na jam'iyyar APC da kuma David Ombugadu na jam'iyyar PDP, kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto.
Idan baku mance ba ranar 15 ga watan Nuwamba, kotun ɗaukaka ƙara ta tanadi hukuncinta a ƙarar da Gwamna Sule ya shigar gabanta yana kalubalantar hukuncin kotun zaɓe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ita dai kotun sauraron kararrakin zabe ta tsige Gwamna Sule kuma ta ayyana ɗan takarar PDP a matsayin sahihin wanda ya ci zaɓen da aka yi ranar 18 ga watan Maris a Nasarawa.
An tsaurara matakan tsaro a faɗin Nasarawa
Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta kara tsaurara matakan tsaro a fadin jihar domin dakile duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya gabanin hukuncin kotun daukaka kara.
Mukaddashin kwamishinan ‘yan sandan jihar, Shettima Muhammad, ya shaidawa yan jarida a Lafiya cewa, an girke dakaru a wasu muhimman wurare a jihar.
Bisa haka ya gargadi jam’iyyun siyasa da magoya bayansu su guji duk wani abu da ka iya tada zaune tsaye ko haifar da tashin hankali a jihar Nasarawa.
"Duk wani mutum ko kungiyar da ta yi kokarin kawo cikas ga zaman lafiya da saɓa wa doka da oda, za su fuskanci fushin doka," in ji shi.
Kotun Abuja ta bada belin tsohon gwamnan CBN
Kuna da labarin Babbar kotun birnin tarayya Abuja, ranar Laraba, ta bada belin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele kan kuɗi N300m.
Alkalin kotun mai shari'a Hamza Mu'azu ya kwace takardun tafiye-tafiyen Emefiele, ya kuma gindaya masa sharuɗɗa masu tssauri.
Asali: Legit.ng