Jagoran NNPP Ya Maida Zazzafan Martani Kan Hukuncin Kotun Daukaka Kara Na Tsige Gwamna Abba
- Jagora kuma wanda ya kafa jam'iyyar NNPP ya maida martani kan hukuncin tsige Abba Gida-Gida da Kotun ɗaukaka ƙara ta yi
- Dakta Boniface Aniebonam, ya bayyana cewa babu mai hurumin kalubalantar zaman Abba mamban NNPP sai ɗan jam'iyya
- Ya roƙi ɗaukacin mambobin NNPP musamman mazauna Kano su ƙara hakuri da wannan jarabawar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Babban jigon siyasa wanda ya kirkiro New Nigeria Peoples Party (NNPP), Dakta Boniface Aniebonam, ya nuna kaɗuwa bisa hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara na tsige Gwamnan Kano.
Ya bayyana hukuncin da Kotun ta yanke ranar Jumu'a 17 ga watan Nuwamba, 2023 a matsayin abin kaɗuwa da takaici, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Da yake martani kan rushe takarar Gwamna Abba Kabir Yusuf da Kotun ta yi, Aniebonam ya jaddada cewa NNPP ce kaɗai ke da ikon tantance mambobinta ba shari'a ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A sanarwan da ya fitar ranar Asabar, babban jigon da ya kafa NNPP, Dakta Aniebonam ya ce:
"Abinda na sani shi ne NNPP da 'ya'yanta ne kaɗai ke da hurumin tantance su waye mambobinta, na san cewa jam'iyya na iya yiwa mutum alfarma, ta tsaida shi takara a zaɓe."
“Haka nan kuma na yi imani cewa wanda ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar NNPP ne kaɗai zai iya kalubalantar kasancewar wani mamban jam’iyyar a zabe. Saɓanin haka babu mai hurumi."
Wanda ya kafa NNPP ya ce jam’iyyar na da ikon daukar nauyin duk wani dan takara ta hanyar yi masa alfarma da ba shi damar tsayawa takara a karkashin inuwarta.
Zamu kwato haƙƙin mu a Kotun koli - Aniebonam
Jagoran NNPP ya kuma bayyana kwarin guiwa da fatan cewa gaskiya za ta yi halinta a Kotun ƙolin Najeriya, Premium Times ta ruwaito.
Ya buƙaci mambobin NNPP da mazauna jihar Kano da su ƙara hakuri da wannan kalubale da ake fuskanta a shari'ar zaɓen gwamna Yusuf.
"Fatan mu na nan yayin da muke tunkarar hukuncin Kotun ƙoli nan ba da jimawa ba," in ji shi.
Gwamnatin Tinubu ta sanar da kuɗin kujerar Hajjin 2024
A wani rahoton kuma Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa Musulmai za su biya N4.5m a matsayin kuɗin kujerar hajji mai zuwa 2024.
Hukumar kula da jin daɗin maniyyata (NAHCON) ce ta sanar da haka a wata sanarwa, ta kuma sanya wa'adin biyan kuɗin.
Asali: Legit.ng