"Siyasar Ubangida": Bidiyon Ododo Duke a Gaban Yahaya Bello Ya Haddasa Cece-Kuce

"Siyasar Ubangida": Bidiyon Ododo Duke a Gaban Yahaya Bello Ya Haddasa Cece-Kuce

  • Yan Najeriya a soshiyal midiya sun caccaki zababben gwamnan jihar Kogi kan kwantar da kai da ya yi yayin gabatar da satifike dinsa na lashe zabe
  • An gano zababben gwamnan, Usman Ododo, duke a gaban ubangidansa, Gwamna Yahaya Bello
  • Jim kadan bayan nan, sai magoya baya a wajen gabatar da satifiket din suka fara rera wakokin yabo ga gwamnan mai ci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Lokoja, Kogi - Dandalin soshiyal midiya ya dauki dumi a ranar Juma'a, 17 ga watan Nuwamba, inda mutane suka yi cece-kuce kan abun da ya wakana yayin gabatarwa zababben gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo takardar shaidar cin zabe.

A cikin bidiyon da ya yadu, an gano Ododo yayin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta gabatar masa da takardar shaidar cin zabe.

Kara karanta wannan

"Allah ya ba ku ikon sauke nauyi", Tinubu ya taya Diri, Ododo, Uzodimma murna

Ododo ya karbi takardar shaidar cin zabe
"Siyasar Ubangida": Bidiyon Ododo Duke a Gaban Yahaya Bello Ya Haddasa Cece-Kuce Hoto: Usman Ododo
Asali: Facebook

Jim kadan bayan nan sai ya isa gaban ubangidansa, Gwamna Yahaya Bello sannan ya durkusa a gabansa, yana mai nuna godiya kan goyon bayan da ya nuna masa a yayin zaben gwamnan da aka kammala kwanan nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An jiyo magoya baya a wajen gabatar da satifiket din suna rera wakar "kai shugaba ne."

Yan Najeriya sun yi martani

Sai dai kuma, sam hakan bai yi wa wasu yan Najeriya dadi ba inda suka bayyana rashin jin dadinsu a kan tabarbarewar damokradiyya a Najeriya.

Wasu mutane sun ga laifin Shugaban kasa Bola Tinubu kan daukaka siyasar ubangida a tsarin siyasar Najeriya na yanzu.

Wata yar Najeriya mai suna @Nairaexchanger a dandalin X, ta rubuta:

"Siyasar ubangida ta samu shahara daga wajen Tinubu da wakilansa a Lagas. Lallai gonar dabobbi ce."

@MissRozapepper ta rubuta:

Kara karanta wannan

INEC ta dage tattara sakamakon zaben gwamnan Bayelsa, cikakken bayani ya bayyana

"Gaba daya laifin a kan Tinubu be. Shi ya samar da siyasar ubangida a Najerita. Kasar nan za ta ci gaba da tabarbarewa, ba tsinuwa bane."

@Nithsmit ta rubuta:

"Wannan shine abun da mutane ke zaba.
"Damokradiyyar Najeriya ta tafi.
"Gaba daya abun da suke iya yi yanzu shine ba iyayen gidansu kudi sannan su murdo su kan mulki, ba sai sun yi maka aiki ko sama maka ababen more rayuwa ba saboda baka da muhimmanci kuma ba kai ka zabe su ba."

@PrisciliaAmadi ta rubuta:

“Ni matar aure ce ya zama gwamna yanzu.
"Ina tayaka murna kan zabenka na sata."

Kalli bidiyon a kasa:

Dino Melaye ya magantu kan siyan kuri'u

A wani labarin, mun ji cewa an zargi Dino Melaye, dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamna da aka yi a ranar 11 ga watan Nuwamba, a jihar Kogi, da siyan kuri'u.

A cikin wani rahoto a ranar Alhamis, 16 ga watan Nuwamba, Sahara Reporters ta yi zargin cewa Melaye, wanda ya zo na uku a zaben, ya fusata sannan ya nemi wasu mambobin jam'iyya a jihar da su dawo masa da kudinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng