Jami'an Tsaro Sun Ɗauki Mataki a Wasu Wurare a Kano Bayan Tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf

Jami'an Tsaro Sun Ɗauki Mataki a Wasu Wurare a Kano Bayan Tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf

  • An girke jami'an tsaro a muhimman wurare domin tabbatar da doka da oda a cikin kwaryar birnin Kano bayan hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara
  • Wannan na zuwa ne bayan tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na NNPP daga matsayin gwamnan jihar Kano ranar Jumu'a
  • Mutanen Kano sun haɗa majalisu suna tattauna tsige Gwamnan amma babu tabbacin ko zai garzaya kotun ƙoli

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Jami'an tsaro sun mamaye muhimman wurare ranar Jumu'a a cikin kwaryar birnin Kano domin daƙile duk wani yunƙurin tada yamutsi da karya doka da oda.

Abba Kabir Yusuf da Nasiru Gawuna.
An Tsaurara Matakan Tsaro a Kano Bayan Kotun Ɗaukaka Kara Ta Tsige Abba Hoto: Abba Kabir Yusuf, Nasir Gawuna
Asali: Facebook

Dakarun tsaron sun ɗauki wannan matakin ne biyo bayan hukuncin da Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na tsige Abba Kabir Yusuf daga matsayin gwamnan Kano.

Kara karanta wannan

'Jarabawa ce, gwamna ya yi martani kan hukuncin kotun da ta rusa zabenshi, ya sha alwashi

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da jihar ta samu kwanciyar hankali kuma kowane ɗan jihar ke ci gaba da gudanar da harkokinsa na yau da kullun a yau Jumu'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Tribune ta tattaro cewa an buɗe manyan kasuwannin cikin birnin Kano kuma mutane sun ci gaba da gudanar da harkokin kasuwanci bayan hukuncin Kotun.

Idan baku manta ba, dama kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Hussaini Gumel, ya gargaɗi mutanen jihar su guji murna mara kan gado idan Kotun ta yi hukunci.

Ya yi wannan gargaɗi ne a wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sanda reshen jihar Kano, SP Haruna Kiyawa, ya fitar gabanin hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja.

Yadda aka girke jami'an tsaro a wasu wurare

Sai dai tun karfe shida na safe jami’an tsaro da suka haɗa da ‘yan sanda da sibil Difens da sauran jami’an tsaro suka mamaye wasu fitattun wurare a jihar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Halin da mutane suka shiga a jihar Kano bayan kotun ɗaukaka ƙara Ta tsige Abba Gida-Gida

An girke dakarun ƴan sanda da sauran jami'an tsaro a babban Titin zuwa Zariya, titin Audu Baƙo, titin Murtala Muhammad da titin Ahmadu Bello Way, Daily Trust ta tattaro.

Haka zalika titin State Road, wanda zai kai ka gidan Gwamnatin Kano, jami'an tsaro sun toshe shi kuma mutane da matafiya sun koma amfani da wata hanyar da zata kai su titin Hotoro.

An ga mutanen jihar sun haɗa majalisa daban-daban suna tattauna hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara, amma ba bu tabbacin ko Gwamna Yusuf zai ƙarisa Kotun ƙoli.

Halin da Mutane Suka Shiga a Jihar Kano

A wani rahoton na daban kuma Iyaye sun shiga tashin hankali da rashin tabbas bayan kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf

Rahotanni sun bayyana cewa wasu iyaye a ƙaramar hukumar Fagge sun garzaya makarantu sun ɗauko 'ya'yansu domin gudun abinda ka iya biyo baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262