Hukuncin Kotun Daukaka Kara: Kwankwaso Ya Aika Gagarumin Sako Ga Abba Gida-Gida

Hukuncin Kotun Daukaka Kara: Kwankwaso Ya Aika Gagarumin Sako Ga Abba Gida-Gida

  • An bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano da ya ci gaba da harkokinsa sannan ya karbi hukuncin kotun daukaka kara
  • Kotun daukaka kara ta tsige gwamnan mai ci a ranar Juma'a, 17 ga watan Nuwamba, inda ta soke nasarar zabensa na ranar 18 ga watan Maris
  • An bukaci Abba Gida-Gida da ya hakura da zuwa kotun koli domin hujjar da ake da shi a kansa ba wanda za a iya watsi da su bane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - Babban jigon jam'iyyar APC, Alhaji Iliyasu Kwankwaso, ya bukaci gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya karbi hukuncin kotun daukaka kara da ta tsige shi daga kujerarsa, rahoton Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da jimamin korarsa a gwamnan Kano, Abba ya tura 'ya'yan talakawa 150 karatu a India

Kotun ta tabbatar da Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin sahihin wanda ya lashe zaben gwamna na ranar 18 ga watan Nuwamba a jihar Kano.

An shawarci Abba ya yarda da shan kaye
Hukuncin Kotun Daukaka Kara: Kwankwaso Ya Aika Gagarumin Sako Ga Abba Gida-Gida Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Kwankwaso, tsohon kwamishinan raya karkara da cigaban al'umma a jihar, ya gargadi Abba Gida Gida a kan ci gaba da bibiyar shari'ar har zuwa kotun koli, musamman bayan shan kaye a kotun zabe da kotun daukaka kara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Leadership ta nakalto yana cewa:

"Zai zama wani babban aiki ja a gare shi ya kai shari'ar kotun Allah ya isa, duba ga hujjojin da aka gabatar kansa a kotun zabe da kotun daukaka kara, akwai bukatar ya je ya huta har zuwa 2027."

Da yake martani ga hukuncin kotun daukaka karar kan takaddamar zaben gwamnan jihar Kanon, Kwankwaso ya yaba ma nasarar dan takarar gwamnan APC, Nasiru Yusuf Gawuna, yana mai nuni da shi a matsayin nasara ga damokradiyya da tsarin doka.

Kara karanta wannan

Jigon NNPP ya yi zazzafan martani kan hukuncin kotun daukaka kara na sauke Abba Gida-Gida

Kwankwaso bai ji dadin abun da Abba Gida-Gida ya yi ba

Kwankwaso ya nuna rashin jin dadinsa cewa Abba Yusuf bai amshi hukuncin kotun zaben gwamna ba kuma maimakon haka sai ya zabi karar da albarkatun kasar wajen bibiyar shari'ar a kotun daukaka kara.

Da soke zabensa da kotun daukaka kara ta yi, Kwankwaso ya bayar da shawarar cewa ya kamata Gwamna Yusuf ya mayar da hankali kan shirin sake takara a 2027 karkashin jam'iyyar siyasa mai tasiri.

Ya ce:

"A matsayina na dan uwa, ina amfani da wannan damar don shawartarsa da ya kau da duk wani yunkuri na jan batun zuwa kotun Allah ya isa amma dai ya kwana da sanin cewa lokaci bai yi ba da zai zama gwamnan jihar."

Malam Saidu Abdu, jigon NNPP a ƙaranar hukumar Nasarawa ta jihar Kano, ya shaida wa Legit Hausa cewa ba zasu rungumi hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara ba.

Kara karanta wannan

Hukuncin kotun daukaka kara: Farfesan arewa ya yi gargadi kan yiwuwar barkewar rikici a Kano

Ɗan siyasan ya bayyana cewa za su tunkari kotun ƙoli domin neman haƙƙinsu a karo na karshe amma dai sun miƙa komai hannun Allah.

Abdu ya ce:

"A'a ba zamu tsaya a iya kotun ɗaukaka ƙara ba, kamar yadda mai girma Gwamna Abba ya yi jawabi, zamu je kotun koli. Shi da yake wannan zance dan ana murɗe hukunci ne a ba su."
"Wallahi ina mamakin wannan abu, ga wanda mutane suka zaɓa amma ana neman kakaba musu wani bisa tilas. Ina da tabbacin idan APC ta ƙarɓi mulkin Kano, mutane da yawa sun gama zaɓe."

Kano: NNPP za ta Kotun Koli

A halin da ake ciki, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ta bayyana bakin cikinta game da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, da ta kori gwamnan Kano, Abba Yusuf.

Jam'iyyar ta ce za ta binciki duk wata hanya ta doka da za ta kwato mata hakkinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng