Kogi: Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Nemi a Biya Shi N250,000 da Ya Rabawa Akwatuna? Gaskiya Ta Bayyana

Kogi: Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Nemi a Biya Shi N250,000 da Ya Rabawa Akwatuna? Gaskiya Ta Bayyana

  • An zargi Dino Melaye, dan takarar PDP a zaben gwamnan jihar Kogi na ranar 11 ga watan Nuwamba, da siyan kuri'u, cewa ya rabawa kowace rumfar zabe N250,000
  • Sai dai kuma dan takarar na PDP ya musanta zargin, yana mai cewa ana kokarin janye hankali ne daga magudin da aka tafka a zaben
  • Melaye, wanda ya zo na uku a zaben, ya nemi a soke zabe a kananan hukumomi biyar, yana mai nuni ga takardun zabe da aka cike tun kafin a kammala zaben

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Lokoja, jihar Kogi - An zargi Dino Melaye, dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamna da aka yi a ranar 11 ga watan Nuwamba, a jihar Kogi, da siyan kuri'u.

Kara karanta wannan

Fani-Kayode ya caccaki Dino Melaye kan kayen da ya sha a zaben Kogi: “Allah Sarki Dino, ya zo na 3”

A cikin wani rahoto a ranar Alhamis, 16 ga watan Nuwamba, Sahara Reporters ta yi zargin cewa Melaye, wanda ya zo na uku a zaben, ya fusata sannan ya nemi wasu mambobin jam'iyya a jihar da su dawo masa da kudinsa.

An zargi Dino da siyan kuri'u yayin zaben gwamnan Kogi
Kogi: Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Nemi a Biya Shi Kudin da Ya Rabawa Akwatuna? Gaskiya Ta Bayyana Hoto: Dino Melaye
Asali: Facebook

Rahoton ya yi ikirarin cewa Melaye, tsohon sanata mai wakiltan Kogi ta yamma, "ya rabawa kowace rumfar zabe N250,000."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kafar yada labaran ta kuma bayyana cewa "rabe-raben kudaden da PDP ta kashe a zaben jihar ya nuna cewa an kashe naira miliyan 87 don "tattara masu kada kuri'a" - wanda aka fi sani da siyan kuri'u".

Ta kuma ambato wasu manyan majiyoyi da ba a bayyana sunayensu ba suna cewa Melaye ya fusata saboda yana zargin wani shugaban karamar hukuma na PDP, Darakta-Janar na kamfen dinsa da wasu da suka gaza kawo masa kuri'u sun damfare shi.

Kara karanta wannan

"Ko na yi zabe ko ban yi ba bai da amfani": Dino Melaye ya magantu kan yadda APC ta murde zaben Kogi

Dino Melaye ya yi martani

Da yake martani ga rahoton Sahara Reporters, Sanata Melaye ya karyata ikirarin ta hannun daraktan yada labaransa.

Ya zargi kafar labaran ta yanar gizo da goyon bayan masu son yi wa damokradiyya zagon kasa.

Dan takarar gwamnan na PDP a Kogi ya karyata zargin siyan kuri'un, yana mai bayyana su a matsayin kokarin janye hankali daga zargin magudin zabe da aka tafka a ranar 11 ga watan Nuwamba.

Sai dai kuma, ya bayyana cewa bai yi mamaki ba, yana mai cewa APC na kokarin yin rufa-rufa ne a kan magudin da aka tafka.

Jigon na PDP ya bukaci mutanen jihar Kogi da su yi watsi da rahoton, yana mai yin fatali da shi a matsayin "farfaganda".

Daraktan yada labaran ya jaddada jajircewar Sanata Melaye ga gaskiya da adalci tare da yin kira ga jam'iyyar APC da ta fuskanci sakamakon damfarar da ake zarginsu da aikatawa maimakon komawa ga fada ta kafofin watsa labarai.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: INEC Ta Ayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Bayelsa

APC na neman a daure Dino

A wani labarin, mun ji cewa jam’iyyar APC ta reshen jihar Kogi ta yi kira ga jami’an tsaro su gaggauta cafke Dino Melaye saboda ana zargin ya aikata laifuffuka.

The Nation ta rahoto APC mai mulki tana mai cewa Sanata Dino Melaye da bakinsa ya fadawa duniya ya aikata laifuffuka ta yanar gizo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng