To Fa: Gwamnan PDP Ya Yi Watsi da Umarnin Kotu, Ya Tsige CJ Ta Jiharsa Ya Naɗa Sabo

To Fa: Gwamnan PDP Ya Yi Watsi da Umarnin Kotu, Ya Tsige CJ Ta Jiharsa Ya Naɗa Sabo

  • Gwamna Adeleke ya kauce wa umarnin Kotun ɗa'ar ma'aikata wadda ta hana shi korar shugabar alƙalan jihar Osun, Oyebola Oyo
  • A wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, Gwamna Adeleke ya dakatar da ita kuma ya naɗa wanda zai maye gurbinta
  • Sanarwan ta bayyana cewa Gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne bayan amincewar majalisar dokokin jihar Osun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Gwamna Ademola Adeleke ya bijirewa umarnin kotun ɗa'ar ma'aikata ta kasa wanda ya dakatar da shi daga tsige babban alkalin jihar Osun, Oyebola Ojo.

Gwamna Adeleke ya dakatar da CJ ta jihar Osun.
Gwamna Adeleke Ya Shure Umarnin Kotu, Ya dakatar da CJ na jihar Osun Hoto: Ademola Adeleke
Asali: Facebook

A ranar Alhamis, 16 ga watan Nuwamba, Gwamna Adeleke na jam'iyyar PDP ya dakatar da mai shari'a Ojo daga matsayin babban alkalin jihar, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta rasa ɗan Majalisa ɗaya tilo da take da shi a jihar Arewa, ya koma APC

Matakin da Gwamnan ya ɗauka na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Olawale Rasheed, ya fitar yau Alhamis a Osogbo, babban birnin Osun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa an ɗauki wannan matakin ne biyo bayan sahalewar majalisar dokoki ta jihar Osun.

Gwamna ya naɗa sabon CJ a Osun

Sanarwan ta ƙara da bayanin cewa Gwamnan ya kuma amince da naɗa mai shari'a Olayinka Afolabi a matsayin sabon muƙadɗashin Alkalin alƙalan Osun (CJ).

"Bisa umarni. Gwamna, mataimakin gwamna zai rantsar da sabon muƙaddashin shugaban alkalan jihar Osun da aka naɗa gobe a gidan gwamnati da ke Osogbo," in ji sanarwan.

Channels tv ta tattaro cewa tun da faro, Kotun ɗa'ar ma'aikata ta ƙasa ta hana Gwamna Adeleke ya tsige mai Shari'a Ojo daga matsayin shugaban alkalan Osun amma ya bijire.

Majalisar Dattawa Ta Tabbatar da Sabon Naɗin da Shugaba Tinubu

Kara karanta wannan

Kotu ta dakatar da gwamnan PDP daga sauke shugabar alkalan jihar, ta ba shi umarni mai tsauri

A wani rahoton na daban kuma Majalisar dattawa ta tabbatar da naɗin Dokta Aminu Maida a matsayin sabon mataimakin shugaban hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC).

A yayin da ake tantance shi, Maida ya shaida wa ‘ yan majalisar cewa idan har aka tabbatar da naɗinsa, zai mayar da hankali ne wajen ingantanhanyoyin sadarwa a sassan kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262