Jam'iyyar Kwankwaso Ta Shiga Tattaunawar Haɗa Maja da Wasu Jam'iyyu? Gaskiya Ta Fito

Jam'iyyar Kwankwaso Ta Shiga Tattaunawar Haɗa Maja da Wasu Jam'iyyu? Gaskiya Ta Fito

  • Jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta nesanta kanta da kowace irin tattaunawar haɗa maja da wasu jam'iyyun siyasa
  • Sakataren watsa labaran NNPP na ƙasa, Alhaji AbdulRazaq AbdulSalam, ya ce matakin da BoT ta ɗauka kan Kwankwaso na nan daram
  • Ya ce suna da labarin an fara neman haɗa maja da wasu jam'iyyu amma NNPP ba ta da sha'awar shiga cikin wannan batun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Lagos - New Nigeria People’s Party (NNPP) ta tabbatar da cewa ba ta shiga tattaunawar dunƙulewa wuri ɗaya da wasu jam'iyyun siyasa ba kuma hakan ba mai yiwuwa bane.

Jam'iyyar NNPP ta musanta shiga tattaunawar haɗa maja.
NNPP Ta Musanta Shiga Tattaunawar Hada Maja da Wasu Jam'iyyun Siyasa Hoto: NNPP
Asali: UGC

Sakataren watsa labaran jam'iyyar NNPP ta ƙasa, Alhaji AbdulRazaq AbdulSalam, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a jihar Legas, The Nation ta rahoto.

“NNPP jam'iyya ce mai zaman kanta, bisa haka muna nan a kan kudurinmu na mutunta dukkan jam’iyyun siyasa kuma ba zamu hada kai ko maja da kowace jam’iyya don yakar wata ba."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta rasa ɗan Majalisa ɗaya tilo da take da shi a jihar Arewa, ya koma APC

"Jam'iyyarmu tana daraja haɗa kai kuma tana kiyaye tsarin da ba na bangaranci ba. Yana da muhimmanci kowa ya san cewa mun kori dukkan masu tattaunawar maja daga NNPP."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mun san cewa a halin da ake ciki NNPP na fama da rigingimun cikin gida gabanin Kotun ta yanke hukunci."

Wane rikici NNPP take fama da shi a cikin gida?

A cewarsa, matakin da kwamitin amintattu (BoT) ya ɗauka na rushe kwamitin gudanarwa karakashin jagorancin Abba Kawu na nan daram.

Haka zalika kakakin NNPP ya bayyana cewa korar da aka yi wa tsohon gwamnan Kano kuma ɗan takararsu na shugaban kasa, Rabi'u Kwankwaso, na nan daram.

A ruwayar Vanguard, Abdulsalam ya ƙara da cewa:

"Muna da masaniyar ana tattaunawar haɗa maja, amma matsayar jam'iyyar NNPP a fili take, ba mu da sha'awar haɗa maja da wata jam'iyya a halin yanzu."

Kara karanta wannan

2027: Peter Obi Sun Shirya Hada Kai da PDP, NNPP Ta Ba Atiku Sharadi Mai Wahala

Gwamnatin Benue ta musanta jifan Gwamna Alia

A wani rahoton na daban Gwamnatin jihar Benue ta karyata rahoton da ke yawo cewa matasa sun jefi Gwamna Alia yayin da ya kai ziyara wata kwaleji a Makurdi.

Sakataren watsa labaran Gwamnan, Sir Kula Tersoo, ya bayyana rahoton da ƙarya wacce aka kirkira da nufin ɓata wa gwamnan suna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262