Reno Omokri Ya Fallasa Gaskiyar Dalilin da Yasa NLC Ta Shiga Yajin Aikin Gama Gari

Reno Omokri Ya Fallasa Gaskiyar Dalilin da Yasa NLC Ta Shiga Yajin Aikin Gama Gari

  • Wani mai sharhi kan harkokin siyasa, Reno Omokri, ya mayar da martani kan yajin aikin da kungiyar kwadago ta ayyana tafiya a fadin kasar
  • Omokri ya ce yan daba sun farmaki shugaban NLC, Joe Ajaero, sannan suka yi masa duka a yayin da yake yiwa jam'iyyar LP kamfen a jihar Imo
  • Jigon na PDP ya ce watakila NLC ta kira yajin aikin gama gari ne saboda rashin jin dadin Ajaero na rasa jiharsa ta Imo

Jihar Imo, Owerri - Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi karin haske kan dalilin da yasa kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta tafi yajin aikin gama gari.

Omokri ya ce shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero, ya yarda cewa wadanda suka farmake shi tare da yi masa duka yan daba ne kuma cewa an sauya kwamishinan yan sandan jihar Imo saboda lamarin.

Kara karanta wannan

NLC Ta Rubutawa Ma’aikatan Wuta, Makarantu Takardar Dunguma Yajin Aiki a Najeriya

Reno Omokrin ya magantu kan yajin aikin NLC
Reno Omokri Ya Fallasa Gaskiyar Dalilin da Yasa NLC Ta Shiga Yajin Aikin Gama Gari Hoto: @renoomokri
Asali: Twitter

Ya ce:

"Babu tunani a gurgunta kasar baki daya saboda wani lamari na mutum daya a wata jiha daya."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai sharhi kan harkokin siyasar ya bayyana hakan ne a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) @renoomokri.

Ya yi zargin cewakasancewar Ajaero a jihar Imo don yi wa dan takarar jam'iyyar LP, Athan Achonu a zaben da aka kammala na gwamnan jihar Imo kamfen ne.

Omokri ya bayyana cewa Ajaero ya kira yajin aikin ne saboda bai ji dadin kayen da ya sha a zaben na jihar Imo ba.

“Ba ma’anaace an gurgunta kasa baki daya saboda wnai abu da ya faru ga mutum daya a jiha daya. Musamman a lokacin da kasancewar a wajen don yi wa dan takarar jam'iyyar LP a zaben da aka kammala a jihar Imo na 2023 kamfen ne. Shin wannan yajin aikin ba don bacin ran Ajaero ya sake rasa jiharsa bane?”

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kungiyoyin Kwadago sun shiga yajin aiki sai baba ta gani kan lakadawa shugaban NLC duka

Kungiyoyin kwadago sun shiga yajin aiki

A wani labarin, Legit Hausa ta kawo a baya cewa kungiyoyin kwadago na Najeriya NLC da TUC, sun umurci mambobinsu da su fara yajin aiki a fadin kasar, sakamakon harin da aka kaiwa shugaban NLC, Joe Ajaero.

Kungiyoyin kwadagon sun umurci dukkanin kungiyoyin ma'aikata da ke karkashinsu, da su tsunduma yajin aikin, bisa umurnin majalisar zartaswa ta kungiyoyin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng