Wakilan APC da Accord Party Sun Bai Wa Hammata Iska a Cibiyar Tattara Kuri’an Zaben Gwamnan Bayelsa
- Wakilan jam'iyyun APC da Accord sun bai wa hamata iska yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben jihar Bayelsa
- Wakilin jam'iyyar Accord Victor Werinepere-Fisi ya naushi takwaransa na APC, Dakta Dennis Otiotio wamda hakan ya jawo dakatar da shirin
- Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben da Gwamna Diri ke kan gaba a zaben
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Bayelsa - Yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben jihar Bayelsa, jam'iyyun APC da Accord sun bai wa hamata iska.
Wakilan jam'iyyun sun doku ne a dakin taron da ake tattara sakamakon zaben inda suka ta da hankulan mutane, cewar Channels TV.
Mene dalilin jawo rikicin tsakanin APC da Accord?
Lamarin ya faru ne a yau Litinin 13 ga watan Nuwamba a Yenagoa babban birnin jihar Bayelsa, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tattara sakamakon wanda mataimakan shugaban Jami'ar Fasaha da ke Minna, Farfesa Faruk Kuta ke jagorancinta an fara ne da misalin karfe 12.
Wannan rikici na wakilan biyu ya kawo cikas a dakin tattara sakamakon zaben wanda sai da aka fitar da su daga ciki.
Wane mataki aka dauka kan rikicin a Bayelsa?
Har ila yau, dalilin wannan rikici an dage ci gaba da tattara sakamakon a wannan lokaci saboda samun daidaito na tsaro, Politics Nigeria ta tattaro.
Wakilin jam'iyyar Accord a jihar, Mista Victor Werinepere-Fisi ya naushi takwaransa na APC, Dakta Denis Otiotio kan rashin jituwa a tsakani.
A yanzu haka an gama tattara sakamakon zaben kananan hukumomin jihar inda Gwamna Douye Diri na jam'iyyar PDP ke ba da ratar kuri'u sama da dubu 65 a zaben jihar.
Sylva ya sake lashe karamar hukuma a Bayelsa
A wani labarin, dan takarar jam'iyyar APC a zaben, Timipre Sylva ya sake lallasa Gwamna Douye Diri a karamar hukumar Brass da ke jihar.
Wannan na zuwa ne bayan Diri na jam'iyyar PDP na bai wa Sylva rata a zaben da aka gudanar a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba.
Asali: Legit.ng