Zaɓen Gwamnan Bayelsa: Cikakken Jerin Ƙananan Hukumomin da PDP, APC Suka Lashe Ya Zuwa Yanzu
- Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ɗage tattara sakamakon gwamnan jihar Bayelsa
- Hukumar zaɓen ta kammala tattara sakamakon ƙananan hukumomi shida cikin takwas na jihar mai arziƙin man fetur
- Gwamna Duoye Diri na PDP na kan gaban Timipre Sylva na APC a sakamakon zaɓen da aka kammala tattarawa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bayelsa - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da dakatar da tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Bayelsa har zuwa ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamba da karfe 12 na rana.
INEC ta fara zaɓen ne a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, a matsayin ɗaya daga cikin zaɓɓukan farko da aka gudanar bayan babban zaɓen 2023 a Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an sanar da dakatarwar ne a cibiyar tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar da ke Yenagoa, babban birnin Bayelsa, a daren Lahadi, 12 ga watan Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Douye Diri, gwamnan jihar Bayelsa kuma ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaben ne ke kan gaba.
Ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Timipre Sylva na biye da shi a zaɓen.
Sakamakon ƙananan hukumomi nawa aka sanar?
Ya zuwa yanzu dai INEC ta fitar da sakamakon ƙananan hukumomi shida cikin takwas na jihar mai arziƙin man fetur a yankin Kudu maso Kudu.
Ga jerin sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin da ƙuri'un da jam'iyyun PDP, APC da Labour Party suka samu:
Ogbia
APC - 16,319
PDP - 18,435
LP - 57
Kolokuma-Okokuma
APC - 5,349
PDP - 18,465
LP - 22
SAGBAMA
APC - 6,608
PDP - 35,504
LP - 217
Yenegoa
APC - 14,534
PDP - 37,777
Nembe
APC - 22,248
PDP - 4,556
LP - 113
Ekeremor
APC - 8,445
PDP - 23,172
LP - 50
Ma'aikaciyar INEC Ta Kuɓuta a Bayelsa
A wani labarin kuma, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), ta bayyana cewa ma'aikaciyarta da aka sace ana jajibirin zaɓen gwamnan jihar Bayelsa ta kuɓuta.
Ebehireme Blessing Ekwe ta kuɓuta ne daga hannun waɗanda suka ɗauke ta a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba bayan kammala kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamnan jihar.
Asali: Legit.ng