Zaben Gwamnan Kogi: Murtala Ajaka Ya Yi Watsi Da Sakamakon INEC, Ya Bayyana Mataki Na Gaba
- Dan takarar gwamna na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a jihar Kogi, Murtala Ajaka, ya ce ba zai tafi kotu don kallubalantar sakamakon zaben ba
- Ajaka, a wani hira na kai tsaye da aka yi da shi a talabijin, ya ce zuwa kotun bata lokaci ne da ba zai haifar da wani amfani ba
- Ya gargadi hukumar zabe cewa idan ta bari magudin zabe da ake yi ya cigaba za ta janyo rushewar doka da oda a kasar
Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe
Jihar Kogi - Dan takarar gwamna na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a jihar Kogi, Murtala Ajaka, ya yi zargin an samu matsaloli a zaben ranar Asabar.
Ajaka ya ce ba zai kallubalanci sakamakon zaben ba a kotu idan bai yi nasara ba domin hakan zai zama bata lokaci ne kawai, Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da ya ke magana da gidan talabijin na Channels a shirin 'The 2023 Verdict: Off Cycle Election', Ajaka ya yi ikirarin magudi aka masa tare da hadin kan Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC).
Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, ya ce:
"Ba tare da raini ga shugaban INEC ba, idan ba su yi bincike kan jami'ansu da suka tafi jihar Kogi ba kuma suka bar wannan abin ya dore, bana tsammanin za a yi zabe a 2027.
"Domin mutane za su shiga zaben ne da makamai, ina fargabar abin da ke faruwa a Somalia zai zama tamkar wasan yara.
"Idan da mun sani cewa abin da aka saba zai faru, mu ma da mun taho da shirinmu mu kara kuri'u daga yankunan mu."
Ajaka ya yi fargabar rushewar doka da oda
Da aka masa tambayan dalilin da yasa ya ke damuwa tunda ba shi da hujjar cewa an yi masa magudin zabe, Ajaka ya ce:
"Me zan tafi kotu in yi tunda INEC da ta aikata wannan abin za ta zo kotu a matsayin mai bada shaida ta kare abin da ta yi? Bata lokaci ne. Sai dai idan yan jam'iyya za su tafi domin ni abin ya bani takaici.
"Ina tabbatar maka idan su (INEC) suka bari wannan abin ya cigaba a sauran jihohi, suna neman doka da oda ya rushe kenan a kasar."
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng