An Shiga Jimami Bayan Wasu ’Yan Bindiga Sun Bindige Shugaban Jam’iyyar Siyasa a Jihar Anambra
- Rahoton da muke samu ya bayyana yadda tsageru suka hallaka shugaba kuma jigon jam'iyyar YPP a jihar Anambra
- An bayyana yadda tsageru suka kashe mutumin yayin da ya hada taron ganawa da wasu jiga-jigan siyasa a jihar
- Ya zuwa yanzu, 'yan sanda basu samu labari ba, amma YPP ta tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
Jihar Anambra - Wasu tsagerun da har yanzu ba a tantance su waye ba sun hallaka jigon jam’iyyar ci gaban matasa ta YPP na gundumar Nanka 1, Joe Mohel.
Nanka wani yanki ne da cikin karamar hukumar Orumba ta Arewa a jihar Anambra, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
An tattaro cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar, jim kadan bayan wata ganawa da mazauna yankin da mamba mai wakiltar mazabar Orumba ta Arewa da ta Kudu, Chinwe Nnabuife.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaushe hakan ta faru?
Majiyoyi a yankin sun ce ganawar na da nasaba da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke da ta bayar da umarnin sake gudanar da zabe tsakanin Nnabuife da dan takarar jam’iyyar PDP na mazabar Orumba ta Arewa da ta Kudu a zaben 2023, Okwudili Ezenwankwo.
An ce marigayin ya shirya ganawar ne a madadin 'yar majalisar wakilai Nnabuife da kuma ‘yan mazabar.
Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:
“An kashe shi ne a daren jiya (Asabar) bayan da ya shirya ganawa tsakanin ‘yar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Orumba ta Arewa da ta Kudu a majalisar wakilai ta tarayya, Chinwe Nnabuife da ‘yan mazabar ta Nanka."
Martanin 'yan sanda da YPP
A cewarsa, mashekan sun zo wurin da suka yi kisan ne da mota kirar Lexus, inda suka yi harbe-harbe kafin daga bisani su hallaka jigon na YPP, rahoton Daily Post.
Da aka tuntubi shugaban YPP na jihar, Moses Obi, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma akwai sarkakiya a bayanan da yake dasu.
Shi kuwa da aka tuntube shi, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Tochukwu Ikenga, ya ce rundunar ba ta samu labarin faruwar lamarin ba.
Aikina yasa Arewa bata kama da wuta ba, Matawalle
A wani labarin, Bello Matawalle, tsohon gwamnan jihar Zamfara, ya ce ba don daukar matakin da ya yi a matsayinsa na daya daga jiga-jigan jihar Arewa maso Yamma ba, da dukkanin yankin Arewa ya kama da wuta.
Matawalle, wanda shi ne karamin ministan tsaro, ya bayyana haka ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Abuja, Daily Trust ta tattaro.
Asali: Legit.ng