Zaɓen Bayelsa: Tashin Hankali Yayin da Ƴan Daba Suka Halaka Mai Goyon Bayan Babbar Jam'iyya
- Wasu ƴan bangar siyasa sun salwantar da ran wani mai goyon bayan ɗaya daga cikin manyan jam'iyyun siyasa a jihar Bayelsa
- George Sibo ya rasa ransa ne lokacin da ƴan daba suka kai farmaki a cibiyar tattara sakamakon zaɓe da ke Twon-Brass
- Ana zargin cewa ƴan daba masu goyon bayan wata jam'iyyar siyasa ce wacce ba ta George ba suka ɗauki ransa ana tsaka da tattara sakamakon zaɓen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bayelsa - Wasu da ake zargin ƴan bangar siyasa ne sun kashe wani mutum mai matsakaicin shekaru wanda ke goyon bayan ɗaya daga cikin manyan jam'iyyun siyasa, mai suna George Sibo, a jihar Bayelsa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an kashe mai goyon bayan jam’iyyar ne a cibiyar tattara sakamakon zaɓe ta hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) da ke Twon-Brass a ƙaramar hukumar Brass ta jihar Bayelsa.
An tattaro cewa wasu gungun jama’a da ake zargin magoya bayan ɗaya daga cikin jam’iyyun siyasa ne da ke gudanar da zaben suka kai wa marigayin hari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu shaidun gani da ido sun shaida wa manema labarai cewa an kai wa marigayin wanda ke goyon bayan ɗaya daga cikin manyan jam'iyyun hari ne a cibiyar tattara sakamakon zaɓen gwamna da ke hedikwatar laramar hukumar a lokacin da ake mika sakamakon zaɓen wasu mazaɓu na mazaɓa ta ll.
An yi Allah wadai da kisan
Da yake mayar da martani kan lamarin, dan majalisa mai wakiltar mazabar Brass, Dokta Daniel Charles, ya bayyana bakin cikinsa kan "mummunan kisan gillar da masu neman mulki suka yi wa wani matashi mai himma da ƙwazo."
Ya kuma buƙaci jami’an tsaro da su gaggauta kama wadanda suka aikata wannan ɗanyen aikin tare da hukunta su.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Bayelsa, CSP Asinim Butswat, ya ce yana jiran cikakken bayani daga kwamandan ƴan sanda na Brass.
Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin jihar Bayelsa mai suna Degison Degiyai kan yadda aka gudanar da zaɓen gwamna a jihar.
Degison ya bayyana cewa an gudanar da zaɓen cikin lumana sai dai a ƴan wasu wurara da aka samu tashin hankali da ba a rasa ba.
Ya bayyana cewa a lokacin yaƙin neman zaɓe an yi asarar rayuka sosai a jihar.
Ma'aikaciyar INEC Ta Kuɓuta
A wani labarin kuma, ma'aikaciyar hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da aka sace a jihar Bayelsa, ta shaƙi iskar ƴanci.
An dai sace Ebehireme Blessing Ekwe ne a ranar Juma'a 10, ga watan Nuwamba ana sauran kwana ɗaya a fara zaɓen gwamnan jihar Bayelsa.
Asali: Legit.ng