Yanzu Yanzu: Ajaka Na SDP Ya Nemi a Soke Zaben Gwamna a Kogi Ta Tsakiya

Yanzu Yanzu: Ajaka Na SDP Ya Nemi a Soke Zaben Gwamna a Kogi Ta Tsakiya

  • Murtala Ajaka, dan takarar jam'iyyar SDP a zaben gwamnan jihar Kogi ya aika kokensa ga hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta
  • Ajaka ya bukaci INEC da ta soke zabe a kananan hukumomi biyar na jihar Kogi
  • Wannan kira da ya yi yana zuwa ne adaidai lokacin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar na 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Kogi - Yayin da ake ci gaba da tattara sakamako daga zaben gwamna na ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, a jihar Kogi, dan takarar SDP ya bukaci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da ta soke sakamakon zabe daga Kogi ta tsakiya.

A wata rubutaciyyar korafi da wakilin SDP, David Edibo, ya gabatarwa baturen zaben jihar, jam'iyyar ta nuna rashin gamsuwa da sakamakon zaben a kananan hukumomi biyar da ke yankin.

Kara karanta wannan

INEC ta dage tattara sakamakon zaben gwamnan Bayelsa, cikakken bayani ya bayyana

Ajaka ya nemi INEC ta soke zaben Kogi ta tsakiya
Yanzu Yanzu: Ajaka Na SDP Ya Nemi a Soke Zaben Gwamna a Kogi Ta Tsakiya Hoto: Murtala Ajaka/Usman Ododo
Asali: Twitter

Gwamna Yahaya Bello da dan takarar APC Usman Ododo sun fito ne daga yankin Kogi ta tsakiya, Channels TV ta rahoto.

A halin da ake ciki, wakilin jam'iyya mai mulki, Idris King, ya yi watsi da korafin jam'iyyar adawar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da sakamakon zaben da ake tattarawa ya fara kaiwa karshe, manyan yan takara a zaben sun hada da Murtala Ajaka (SDP), Leke Abejide (African Democratic Party), Dino Melaye (Peoples Democratic Party), da Usman Ododo (APC).

Dino ya nemi a soke zaben Kogi ta tsakiya

Hakan na zuwa ne bayan dan takarar gwamnan jam'iyyar PDP a jihar Kogi, Sanata Dino Melaye, ya yi kira ga hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da ta soke zabe a kananan hukumomi biyar na jihar.

Melaye ya ce zaben da aka gudanar a wadannan yankuna na cike da magudi na fitar hankali.

Kara karanta wannan

Labari Mai Zafi: SDP Ta Doke APC a Karamar Hukumar Farko da INEC ta Sanar a Kogi

Tsohon dan majalisar tarayyar ya lissafa kananan hukumomin da yake son a soke zabe a matsayin Okene, Okehi, Ajaoukuta, Adavi, da Ogori/Mangogo – gaba dayansu a yankin Kogi ta tsakiya.

Da yake kiran a dandalinsa na X, Dino ya ce: "Ya zama dole INEC ta soke zabe a kananan hukumomi 5 na Kogi ta tsakiya. Zaben da aka yi a Okene, Okehi, Ajaoukuta, Adavi, da Ogori/Mangogo duk suna cike da zamba na fitar hankali."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng