PDP Ta Lashe Karamar Hukuma Ta Farko Yayin da INEC Ta Fara Tattara Sakamakon Karshe a Bayelsa
- Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta fara tattara sakamakon karshe a zaben gwamnan jihar Bayelsa na 2023
- Dan takarar jam'iyyar PDP, Duoue Diri ya samu gagarumar nasara wajen lashe karamar hukumarsa ta Kolokuma/Opokuma
- Yan takara 15 suka fafata da Gwamna Duoye Diri a zaben na ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba
Jihar Bayelsa, Yenagoa – Jam’iyyar PDP a jihar Bayelsa ta samu gagarumar nasara ta farko a karamar hukumar gwamnan jihar kuma dan takarar gwamna, Douye Diri.
Jam'iyyar mai mulki a jihar ta lallasa abokiyar adawarta wato APC da kuri'u 18, 465 .
Yayin da APC ta samu kuri'u 5,349, jam'iyyar Labour Party (LP) ta samu kuri'u 22.
A halin da ake ciki, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta fara tattara sakamakon karshe a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa kuma nan ba da dadewa ba za a sanar da wanda ya lashe zaben.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya takara da jam'iyyun siyasa 16 ne suka yi takara a zaben gwamnan na ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, 2023.
Gwamna mai ci kuma dan takarar PDP, Diri wanda ke neman zarcewa kan kujerarsa ya fafata da yan takara 15 ciki harda Timipre Sylva na APC da Udengs Eradiri na jam'iyyar LP.
Amma a yadda ake ciki yanzu, Diri ne kan gaba a wasu kananan hukumomi daga sakamakon da aka sanar zuwa yanzu.
Kalli yadda sakamakon yake daki-daki daga karamar hukumar gwamnan a kasa:
Kolokuma/Opokuma LGA da karfe 11:28:
APC - 5,349
LP - 22
PDP - 18, 465
An sako jami'in INEC da aka sace a Bayelsa
A wani labarin, mun ji cewa wani ma’aikacin hukumar INEC da aka yi ram da shi a ranar jaji-birin zaben Gwamnan jihar Bayelsa, ya samu ‘yanci.
Wannan jami’i na SPO ya kubuta daga hannun wadanda ake zargin sun yi awon gaba da shi, Vanguard ta fitar da labarin nan a jiya.
Shugaban sashen wayar da kan masu zabe da kuma harkar yada labarai, Wilfred Ifogah ne ya fitar da wata sanarwa ta musamman. Mista Wilfred Ifogah ya shaidawa manema labarai cewa jami’in ya shaki iskar ‘yanci.
Asali: Legit.ng