Uzodimma Ya Lashe Zabe a Dukkan Kananan Hukumomi 27 Yayin Da INEC Ta Kammala Tattara Sakamako

Uzodimma Ya Lashe Zabe a Dukkan Kananan Hukumomi 27 Yayin Da INEC Ta Kammala Tattara Sakamako

Owerri, Jihar Imo - Gwamnan jihar Imo kuma dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben gwamna da aka gudanar, Hope Uzodimma, ya lashe zabe a kananan hukumomi 27 na jihar.

A cigabar tattara sakamakon zabe na hukumar zabe mai zaman kanta da ke Owerri, babban birnin jihar, Uzodimma ya lashe zabe a dukkan kananan hukumomin jihar kamar yadda INEC ta sanar, Premium Times ta rahoto.

INEC ta tafi hutu na awa daya kafin sanar da wanda ya lashe zaben Imo

A yayin tattara sakamakon na karshe a safiyar ranar Lahadi, baturen zabe na jihar, Farfesa Abayomi Fasina, wanda shine shugaban jami'ar Oye, Ado Ekiti, ya sanar da zuwa hutu na awa daya domin ya samu damar kidaya sakamakon sannan ya sanar da wanda ya lashe zaben.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Imo na 2023: Yar yi wa kasa hidima dauke da BVAS da sakamakon zabe ta bace

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel