Zaben Kogi: Ɗan Takarar Gwamnan PDP Ya Lashe Rumfar Zaɓensa, Sakamako Ya Fito

Zaben Kogi: Ɗan Takarar Gwamnan PDP Ya Lashe Rumfar Zaɓensa, Sakamako Ya Fito

  • Ɗan takarar Gwamna a inuwar jam'iyyar PDP ta fara ƙafar dama yayin da aka fara kidaya kuri'u da sanar da sakamako a matakin rumfunan zaɓe
  • Sanata Dino Melaye ya samu nasara a akwatun zaɓen da yake kaɗa kuri'a da ke yankin ƙaramar hukumar Ijumu a jihar Kogi
  • Tsohon mamban majalisar dattawan ya samu ƙuri'u 210 inda ya yi kaca-kaca da babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC, wanda ya samu kuri'u 22

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Sanata Dino Melaye, ɗan takarar gwamnan jihar Kogi a inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya samu nasarar lashe rumfar zaɓen da yake kaɗa kur'a.

Sanata Dino Melaye.
Zaben Kogi: Ɗan Takarar Gwamnan PDP Ya Lashe Rumfar Zaɓensa, Sakamako Ya Fito Hoto: Dino Melaye
Asali: Facebook

Tsohon mamban majalisar dattawan ya lallasa jam'iyyar APC da gagarumin rinjaye a rumfar zaɓensa da ke Iluafon quarters, RA: Aiyetoro 1, ƙaramar hukumar Ijumu a jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Zaben Kogi: Abu ya fara tsami, Dino Melaye ya kauracewa zaben, ya fadi dalilai masu rikitarwa

Sanata Melaye ya samu ƙuri'u 210 a zaben da aka kaɗa yau Asabar a rumfar zaɓen inda ya lalllasa babban abokin adawarsa na jam'iyyar APC, Usman Ododo, wanda ya samu kuri'u 22.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga yadda sakamakon zaben ya nuna a akwatun Iluafon quarters, RA: Aiyetoro 1, ƙaramar hukumar Ijumu, jihar Kogi.

PDP - 210

APC - 22

ADC - 7

PRP - 2

SDP - 1

NRM - 1

ADP - 1

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin Dino Melaye ya kauracewa zaben jihar Kogi amma ya fito ya karyata rahoton.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa ba a ga Dino ya je rumfar zaɓensa ya kaɗa kuri'a ba yayin da zaɓen Gwamna ke gudanar yau Asabar 11 ga watan Nuwamba.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262