Jihar Imo 2023: Yan Daba Sun Afkawa Jami'an APC Da Ke Siyan Kuri'u, Sun Kwace Musu Miliyan 1.5

Jihar Imo 2023: Yan Daba Sun Afkawa Jami'an APC Da Ke Siyan Kuri'u, Sun Kwace Musu Miliyan 1.5

  • Wasu gungun 'yan daba da ake yi wa lakabi da dabar Daredevil, sun far wa wakilan jam'iyyar APC a cocin All Saints Anglican, Egbu, jihar Imo
  • Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan daban sun bude wuta, tare da yin harbi kan mai uwa da wabi, lamarin da ya tilasta masu zabe da 'yan sanda tsere wa
  • Wannan ya ba 'yan dabar damar kwashe naira miliyan daya da dubu dari biyar na jami'an jam'iyyar da su ke amfani da su wajen siyen kuri'u

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Imo - A ranar Asabar din nan ne ‘yan dabar Daredevil, suka far wa wakilan jam’iyyar APC a cocin All Saints Anglican, Egbu, inda suka yi awon gaba da sama da naira miliyan daya da rabi.

Kara karanta wannan

Zaben Imo 2023: Fada ya barke yayin da INEC ta fara tattara sakamakon zabe

‘Yan ta’addan sun shiga harabar cocin, da ke dauke da rumfunan zabe hudu, yayin da suke harbe-harbe tare da neman kudi daga jami’an APC.

Akwatin Zabe
Yan dabar sun samu damar yin awo gaba da Naira Miliyan 1.5 yayin da su ka fara harbe-harbe Hoto: INEC
Asali: UGC

LEADERSHIP ta samu rahoton yadda mutane da suka hada da ‘yan sanda da ‘yan jarida suka rinka gudu-gudu don tseratar da ransu, a yayin da 'yan dabar ke harbin kan mai uwa da wabi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda 'yan dabar su ka kai farmakin

Wani mai kada kuri’a, Okey, ya shaida wa LEADERSHIP cewa ‘yan dabar sun shiga harabar majami'ar ne kamar masu jefa kuri’a, sai kawai suka ba shammaci mutane ta hanyar zare makaman da ke jikinsu, yayin da ‘yan sanda suka ranta a na kare.

Ya ce:

“Mun gama korafin rashin amincewar mu ga wakilin APC, a lokacin da ya nemi mu sayar masa da kuri'unmu, ana cikin haka ne 'yan daban suka shigo, inda suka bukaci a ba su kudin da za a raba, wasa wasa dai, su ka ciro bindigogi, suka fara harbi, kowa ya yi ta kansa, su ka arce da kudin."

Kara karanta wannan

Labari Mai Zafi: DSS da EFCC Sun Dura Rumfar da Dino Melaye Zai Dangwala Kuri’a

An yi awon gaba da jami'an INEC a ihar Imo

Kun ji yadda aka samu hatsaniya a makarantar firamare ta garin Umuodu, Ezinihitte Mbieri, a karamar hukumar Mbaitoli ta jihar Imo, wurin da ake tattara sakamakon zaben gwamnan jihar da ake yi, yayin da wasu ‘yan siyasa suka yi awon gaba da jami’an zabe da takardun rubuta sakamakon zabe.

Wakilinmu wanda ya bi diddigin lamarin, ya lura cewa an fara samun matsala ne bayan da jami’an hukumar zabe ta INEC, suka sanar da kuri'un da kowace jam’iyya ta samu a rumfar 015 da 016, ba tare da sun shigar da hakan a cikin takardar sakamakon zaben ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.