Zaben Gwamnan Kogi na 2023: Jerin Sunayen Jam’iyyun Siyasa 18 da Yan Takararsu

Zaben Gwamnan Kogi na 2023: Jerin Sunayen Jam’iyyun Siyasa 18 da Yan Takararsu

Jihar Kogi - Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta tantance jimillar yan takara 18 domin fafatawa a zaben gwamna na ranar 11 ga watan Nuwamba a jihar Kogi.

Yan takarar suna fafutuka don karbar mulki daga hannun Gwamna Yahaya Bello mai ci a watan Janairun 2024.

Manyan yan takara a zaben gwamnan jihar Kogi
Zaben Gwamnan Kogi na 2023: Jerin Sunayen Jam’iyyun Siyasa 18 da Yan Takararsu Hoto: Alhaji Ahmed Usman Ododo/Murtala Yakubu Ajaka/Dino Melaye
Asali: Facebook

Manyan yan takara a zaben sune, Usman Ahmed Ododo na jam'iyyar APC, Yakubu Muritala na jam'iyyar SDP da Sanata Dino Melaye na jam'iyyar PDP.

Sai dai kuma, dukka yan takara 18 za su kasance a kan takardar zaben a ranar Asabar, a dukka rumfunar zabe a fadin jihar, kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto.

Ga jerin sunayen yan takarar da jam'iyyunsu a kasa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Abin da ya faru bayan an sace daliban Jami'ar Zamfara – Matawalle ya magantu

  1. Hon. Leke Abejide - African Democratic Congress (ADC)
  2. Sanata Dino Melaye - Peoples Democratic Party (PDP)
  3. Musa Salihu Mubarak - New Nigerian Peoples Party (NNPP)
  4. Okeme Adejoh - Labour Party
  5. Usman Ahmed Ododo - All Progressives Congress (APC)
  6. Jubril Usman Oyibe - Accord Party
  7. Braimoh Olayinka Adenehon - Action Alliance (AA)
  8. Achimugu Augustine Abu - African Action Congress (AAC)
  9. Sunday Frank Onoja - Action Peoples Party (APP)
  10. Dauda Utenwojo - Allied Peoples Movement (APM)
  11. Ilonah Idoko Kingsley - All Progressives Grand Alliance (APGA)
  12. Julius Elukpo - Action Democratic Party (ADP)
  13. Mohammed Kabir Umar - Boot Party
  14. Dirisu Bala Abdulgafar - National Rescue Movement (NRM)
  15. Abdullahi Bayawo - Peoples Redemption Party (PRP)
  16. Omale Samson Agada - Young Progressive Party (YPP)
  17. Suleiman Taiye Fatimah - Zenith Labour Party (ZLP)
  18. Yakubu Muritala Ajaka - Social Democratic Party (SDP)

"Ni matar aure ce", Ododo na APC

Kara karanta wannan

“Ni matar aure ce”: Ododo, dan takarar APC a Kogi ya yi barambarama yayin da yake shagube ga Dino

A wani labarin, mun ji cewa an gano Usman Ododo, dan takarar gwamnan jam’iyyar APC a zaben ranar Asabar da za a yi a jihar Kogi a cikin wani bidiyo yana yin barambarama yayin da yake jawabi ga taron jama’a inda ya kira kansa da “matar aure”.

Ana zargin cewa dan takarar gwamnan na APC yana kokarin yin shagube ne ga babban abokinb hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Dino Melaye, wanda bai da aure.

A dan gajeren bidiyon, an jiyo Ododo yana cewa: "Muna so mu baku tabbacin cewa Ni, Ahmed Usman Ododo, ni matar aure ce, ina da kamun kai."

Wani mai suna Morris Monyo ne ya wallafa bidiyon dan takarar na APC a Twitter a ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng