Zaben Kogi: "Na Tsallake Rijiya da Baya a Hare-Hare 30" Dan Takarar Gwamnana SDP
- Murtala Ajaka ya yi ikirarin cewa ya tsallake rijiya da baya a hare-haren kisan da aka kai masa sau 30 a jihar Kogi
- Ajaka, ɗan takarar Gwamna a inuwar jam'iyyar SDP ya ce harin da aka kai gidan DG na kamfen dinsa, ya lakume rayuka sama da 20
- Ya kuma yi kira da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga tsakani domin a daina kashe magoya bayansa
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kogi - Dan takarar gwamnan jihar Kogi a karkashin inuwar jam’iyyar SDP, Murtala Ajaka, ya ce ya tsallake rijiya da baya har sau 30 tun lokacin da ya shiga takara.
Ya bayyana cewa mutane 23 ne suka rasa rayukansu ranar Talata ciki har da ƴan sanda biyu a gidan darakta Janar ɗinsa, gidan da ya so zuwa ya kwana a wannan rana.
Ajaka ya aike da saƙo ga shugaba Tinubu
Sakamakon haka, Ajaka ya roƙi shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga tsakani don kawo karshen kisan da ake wa magoya bayansa, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma yi kira da shugabannin hukumomin tsaro da ke zaune a Abuja da su binciki irin ayyukan da jami'ansu ke yi a jihar Kogi, yana mai zargin cewa sun bar tushen aikinsu.
Murtala Ajaka ya yi wannan jawabi ne a wurin wani taron manema labarai da ya gudanar a ofishin yaƙin neman zaɓensa da ke Abuja.
Ya kuma ƙara da cewa zasu yi duk mai yiwuwa su tabbatar da ƴan sanda uku da aka kashe a wannan kazamin harin sun samu adalci, Channels tv ta ruwaito.
Ɗan takarar SDP ya ce:
"Sa'o'i biyu aka shafe ana tafka ɓarna a harin da aka kai gidan daraktan kamfem ɗina, 'yan sanda biyu da wasu mutane 20 ne suka rasa rayuwarsu."
"An canza tunanin shugabannin hukumomin tsaro, yanzu suna kallon magoya bayan mu har da DG na kamfe a matsayin ƴan daba."
"Ni suke son su kaahe, na tsallake rijiya da baya a hare-hare 30, idan ba don taimakon Allah ba, kashe ni zasu yi kafin ranar zaɓe."
Guguwar Sauya Sheƙa Ta Mamaye PDP
A wani rahoton na daban Jam'iyyar PDP reshen jihar Ebonyi ta ƙara rasa manyan jiga-jigai da ƙusoshinta waɗanda suka tabbatar da ficewa daga jam'iyyar.
Tsohon mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar, Odefa Obasi Odefa na cikin waɗan da suka miƙa takardar barin PDP.
Asali: Legit.ng