"Yana Tunanin Waye Shi?": Ƴan 'Obidients' Sun Koma Caccakar Peter Obi Kan Wani Abu 1

"Yana Tunanin Waye Shi?": Ƴan 'Obidients' Sun Koma Caccakar Peter Obi Kan Wani Abu 1

  • Wasu daga cikin magoya bayan Peter Obi, ɗan takarar jam'iyyar Labour a zaben shugaban kasa na 2023, sun soke shi kan kalaman da ya yi kan hukuncin kotun ƙoli
  • Peter Obi, a wani taron manema labarai, ya yi Allah wadai da hukuncin kotun ƙoli, sannan ya bukaci magoya bayansa da su dakatar da tafiyar har sai zaɓe mai zuwa
  • Sai dai, a wata tattaunawa a Twitter, magoya bayan Obi, wadanda aka fi sani da 'Obidients', sun caccake shi saboda amincewa da ya yi ya zama ɗan adawa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Magoya bayan Peter Obi, wadanda aka fi sani da 'Obidients', sun sha suka kan sukar da suka yi masa saboda amincewa da hukuncin da kotun ƙoli ta yanke wanda ya tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Datti Baba-Ahmed abokin takarar Obi ya bukaci Tinubu da Shettima su yi murabus, ya bayyana dalilansa

A baya kotun ƙolin ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaben shugaban ƙasa ta yanke wanda ya tabbatar da Shugaba Tinubu a matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa, tare da yin watsi da ƙarar Obi, ɗan takarar LP a zaɓen.

An caccaki magoya bayan Peter Obu
An caccaki magoya bayan Peter Obi kan sukar da suka yi masa Hoto: Peter Obi
Asali: Twitter

Sai dai, a martanin da tsohon gwamnan na jihar Anambra ya yi kan hukuncin kotun kolin ya yi Allah wadai da hukuncin inda ya kara da cewa shi da jam’iyyar Labour da “Ƴan tafiyar 'Obidients' sun kasance ƴan adawa a yanzu”.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Omojuwa ya mayar da martani kan sukar Obi da ƴan 'Obidients' suka yi

Sai dai, a wata tattaunawa a Twitter da magoya bayan Obi suka yi kan taron manema labarai da ya yi, sun caccaki tsohon gwamnan saboda rashin tuntubar su da kuma amincewa da zama ɗan adawa.

Kara karanta wannan

Hukuncin kotun koli: An ba Peter Obi shawarar abin da ya kamata ya yi wa Shugaba Tinubu

JJ Omojuwa, wanda ya sanya faifan sautin muryar ɗaya daga cikin ƴan 'Obidients' a shafinsa na Twitter, ya bayyana cewa:

"Ƴan 'Obidients' sun fara tambayar Peter Obi "yana tunanin shi waye ne? Ina fatan wannan abu ba zai kai su lakaɗa masa duka ba”.

Obidients sun koka da kalaman Peter Obi bayan hukuncin kotun ƙoli

An ji muryar wata tana kuka yayin da take yin Allah wadai da kalaman da Peter Obi ya yi kan amincewa da zama ɗan adawa, ta ce ta sanya rayuwarta cikin kasada kuma ta yi mamakin dalilin da ya sa tsohon gwamnan ya amince ya zama ɗan adawa.

"Za a yi mamaya nan ba da daɗewa ba a Najeriya, kuma wani yana cewa in yi ƙaura, daga ina zuwa ina? A ɗaga juyin juya halin zuwa wace shekarar?"

"Shin yana ganin na sanya rayuwata cikin kasada tun daga bara na shiga zaɓe sannan na fito na ce komai ya wuce? Yana tunanin shi waye ne da zai zo ya ce na ɗage juyin juya hali."

Kara karanta wannan

"Ba zan taba daina kiran Tinubu dillalin kwayoyi ba", Datti Baba-Ahmed ya bayar da dalili

Martanin ƴan Najeriya bayan 'Obidients' sun caccaki Peter Obi

Sai dai, wasu ƴan Najeriya sun garzaya sashen sharhi na wallafar da Omojuwa ya yi, inda suka yi Allah wadai da abin da suka bayyana a matsayin wani tsatsauran ra'ayi daga magoya bayan Peter Obi.

Ga wasu daga ciki:

Femi Yekinni ya ce ana sa ran irin wannan martani daga ƴan tafiyar 'Obidients'

A kalamansa:

"Koda yaushe mun san cewa wannan rana za ta zo, nan ba da jimawa ba za su nemi ya mayar musu da duk gudunmawar da suka aika masa."

Ubakor Gerald ta bayyana cewa Obi ya hau dokin tsattsauran ra'ayi ne domin samun farin jini a zaɓen, yanzu ga hatsarin ya fara bayyana.

A kalamanta:

"Wannan shi ne hatsarin da ke tattare da amfani da aƙidu masu tsattsauran ra'ayi domin samun muƙamin siyasa."
"Sau da yawa yana haifar da rikici da hargitsi. A bayyane yake mai maganar ta bar shiri tun rani."

Kara karanta wannan

Nasarar Tinubu: Peter Obi ya yanke shawara kan sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027

"Obi ya san hatsarin da ke cikin abin da yake yi amma mulki shine kawai damuwarsa."

An Peter Obi Shawara

A wani labarin kuma, an ba Peter Obi shawarar abin da ya kamata ya yi wa Shugaba Tinubu bayan hukuncin kotun ƙoli.

Wahab Shittu ya buƙaci ɗan takarar na jam'iyyar Labour Party da ya ta ya Shugaba Tinubu murnar nasarar da ya samu a kotun ƙoli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel