Datti Baba-Ahmed Abokin Takarar Obi Ya Bukaci Tinubu da Shettima Su Yi Murabus, Ya Bayyana Dalilansa
- Datti Baba-Ahmed na ganin cewa bai kamata Shugaba Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima su cigaba da mulkin ƙasar nan ba
- Abokin takarar na Peter Obi ya buƙace su da su yi murabus saboda an rantsar da su ta hanyar da ta saɓa doka
- Datti ya yi nuni cewa a matsayinsu yanzu na ƴan adawa ba za su yi aiki da gwamnatin Tinubu ba saboda haramtacciya ce
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi
FCT, Abuja - Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour a zaɓen shugaban lasa na 2023, Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima da su yi murabus.
Datti Baba-Ahmed ya bayyana cewa rantsuwar da aka yi musu ta saɓa kundin tsarin mulkin ƙasar nan, cewar rahoton Daily Trust.
Baba-Ahmed ya ce kamata ya yi a bar shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya sake gudanar da zaɓen shugaban ƙasa bayan Tinubu da Shettima sun yi murabus.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yi wannan kiran ne a wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Arise yayin da yake amsa tambayoyi kan yiwuwar yin aiki da gwamnatin Tinubu.
Tsohon ɗan majalisar ya bayyana cewa, an rantsar da Tinubu da Shettima bisa maguɗi bayan zaɓen shugaban kasa na 2023, inda ya kara da cewa jam’iyyar LP ba za ta hada kai da abin da ya bayyana a matsayin "haramtacciyar gwamnati ba".
Meyasa Datti yake so Tinubu da Shettima su yi murabus?
A kalamansa:
"Kotun zaɓe da kotun ƙoli ba su tabbatar da nasarar shugabancin Tinubu ba, sun amince da rashin bin kundin tsarin mulki a zaɓen, kuma suna farin ciki a cigaba da kasancewa a haka. Kuma suna da iko, babu wanda zai iya yin komai akai."
"Shiyasa muka ce wannan nuna ƙarfi ne da bai dace ba. Idan da akwai wani abu da za mu iya yi, da mun dakatar da shi, amma mu ƴan ƙasa ne masu bin doka da oda, shi ya sa nake nan zaune tare da ku a yau kuma har yanzu ina ƙorafi."
"Shin Tinubu da Shettima za su iya yin murabus kawai su bar shugaban majalisar dattawa ya sake gudanar sa wani zaɓe? An rantsar da su ne ta haramtacciyar hanya, sannan ba za mu yi aiki da haramtacciyar gwamnati ba. Idan har ta saɓa wa kundin tsarin mulki, babu ruwan mu da ita."
Tinubu Dillalin Ƙwayoyi Ne, Datti Baba-Ahmed
A wani labarin kuma, Datti Baba-Ahmed ya bayyana cewa ba zai taɓa daina kiran Shugaba Tinubu a matsayin dillalin ƙwayoyi ba.
Datti ya yi nuni da cewa zai girmama Tinubu ne kawai saboda shekarunsa amma hakan ba zai sanya ya daina kiran shi da dillalin ƙwayoyi ba.
Asali: Legit.ng