Hukuncin Kotun Koli: An Ba Peter Obi Shawarar Abin da Ya Kamata Ya Yi Wa Shugaba Tinubu

Hukuncin Kotun Koli: An Ba Peter Obi Shawarar Abin da Ya Kamata Ya Yi Wa Shugaba Tinubu

  • An bukaci ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi, ya taya Shugaba Bola Ahmed Tinubu murna
  • Wahab Shittu, babban lauyan Najeriya (SAN), ne ya yi wannan roƙo a ranar Litinin, 6 ga Nuwamba
  • Ya kuma buƙaci tsohon gwamnan na jihar Anambra da ya guji suka kuma ya rungumi ɗabi'ar yarda da ƙaddara

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

FCT, Abuja - Wahab Shittu, babban lauyan Najeriya (SAN), ya ba Peter Obi, ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023 shawara.

Shittu ya ba da shawarar cewa maimakon ya soki nasarar da Shugaba Bola Tinubu ya samu bayan da kotun koli ta tabbatar da hakan a ranar 26 ga Oktoba, 2023, Obi ya kamata ya taya shi murna.

Kara karanta wannan

Kungiyar SERAP za ta shigar da kara kan Shugaba Tinubu da Gwamna Uzodinma kan abu 1

An bukaci Peter Obi ya ta ya Tinubu murna
An shawarci Peter Obi ya ta ya Tinubu murna Hoto: Mr. Peter Obi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Mista Obi ya ce hukuncin ya tarwatsa ƙwarin guiwar da ƴan Najeriya ke da shi a ɓangaren shari'a na cewa zata kwato masu haƙƙinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A nasa martanin, Shittu, a lokacin da wata hira da gidan talabijin na Channels TV, a shirin 'Politics Today', ya buƙaci Obi da ya rungumi ɗabi’ar ƴan wasa, ya kuma amince cewa a kowace gasa akwai wanda zai yi nasara akwai wanda kuma zai yi akasin hakan.

A kalamansa:

"A gasa, dole ne a sami wanda ya yi nasara, dole ne kuma a sami wanda ya yi rashin nasara. A matsayinka na ɗan wasa, ya kamata ka iya yarda da shan kashi lokacin da ka sha kashi. Mista Peter Obi ba na biyu ya zo amma na uku."
"Ya shigar da ƙorafinsa a kotu, ya yi rashin nasara. Ya sake ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙoli, ya yi rashin nasara. Ina ganin abin da ake bukata a gare shi shi ne ya fito fili ya taya wanda ya yi nasara murna, haka ya kamata ɗan dimokradiyya ya yi.”

Kara karanta wannan

"Ba zan taba daina kiran Tinubu dillalin kwayoyi ba", Datti Baba-Ahmed ya bayar da dalili

Dalilin da ya sa kotun ƙoli ta yi watsi da karar Obi

A kwanakin baya ne kotun koli ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar da Obi da Atiku Abubakar, ɗan takarar jam’iyyar PDP suka yi, inda ta bayyana cewa ƙorafe-ƙorafen da ake a kan zamba, da karya dokokin zabe, da kuma cancantar Tinubu na tsayawa takarar shugaban kasa ba su da wata cancanta.

Shittu ya jadadda cewa duk da cewa an yarda da sukar hukunce-hukuncen kotu, irin wannan sukar ya kamata a dogara ne a kan cancantar hukuncin.

Babban Lauyan ya ce:

“Duk wani hukunci da kotu za ta yanke za a iya suka amma abin tambaya shi ne ta yaya kuke sukar hukuncin kotun? Za ku iya sukar irin wannan hukunci ne a kan gaskiya."

Peter Obi Ya Magantu Kan Sake Yin Takara

A wani labarin kuma, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya yi magana kan yiwuwar ya sake tsayawa takara.

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya ayyana cewa yanzu ya fara tafiyar siyasa, alamar da ke nuna burinsa na kwace mulki hannun Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng