Jerin Sunaye: Gwamna Ya Shige Gaba, Ya Naɗa Shugabannin Kananan Hukomomi 17 da Mataimakansu
- Gwamna Alex Otti na jihar Abiya ya naɗa shugabannin da zasu jagoranci kananan hukumomi 17 da ke faɗin jihar
- Kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin masarautu, Prince Uzo Nwachukwu ne ya bayyana haka a wata sanarwa
- Ya ce tuni aka tura sunayen mutanen ga majalisar dokokin jihar Abia domin tantance su da tabbatar da naɗinsu
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Abia - Gwamnan jihar Abiya da ke Kudu maso gabashin Najeriya, Dokta Alex Otti, ya naɗa sabbin shugabannin kananan hukumomi da mataimakansu na rikon kwarya.
Kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautu, Prince Uzo Nwachukwu, ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Talata, Vanguard ta ruwaito.
Ya ce gwamnan ya aika sunayen waɗan da aka naɗa zuwa majalisar dokokin jihar Abiya domin tantancewa da tabbatar da su kamar yadda doka ta tanada, Channels tv ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta tattaro muku sunayen waɗanda Gwamnan ya nada, ga su kamar haka:
Karamar hukumar Isiala Ngwa ta kudu
Ciyaman- Dakta Elelenta Nwabuisi Elele
Mataimaki- Mista Eberechukwu Ahuruonye
Karamar hukumar Ukwa ta yamma
Ciyaman- Mista Newman Azu
Mataimaki - Mista Anele Michael
Karamar hukumar Arochukwu
Ciyaman - Cif Joe Ezearu
Mataimaki - Mista Okezie Azuma
Karamar hukumar Umuahia ta kudu
Ciyaman - Mista Obike Ejike Nnochiri
Mataimaki - Mista Olendingwa Nwabueze
Karamar hukumar Isiala Ngwa ta arewa
Ciyaman- Mr. C. Y. Nwankwo.
Mataimaki - Mr. Uchenna Nwanbuko.
Ƙaramar hukumar Umunneochi
Ciyaman - Mr. Ndubuisi Ike
Mataimaki - Mr. Njoku Augustine C
Karamar hukumar Isuikwuato
Ciyaman - Air Vice Marshal Chinwendu Onyike (mai ritaya)
Mataimaki - Honorabul Harrison Onuke
Ƙaramar hukumar Ikwuano
Ciyaman - Mr. Osinachi Hycinth Nwaka
Mataimaki - Chief Charles Ugbuajah
Karamar hukumar Bende
Ciyaman - Barista Chijioke Nwankwo
Mataimaki - Mr. Onyedikachi Iroegbu.
Ƙaramar hukumar Ohafia
Ciyaman - Chief David Ogba
Mataimaki - Honorabul Mkpa Oju Uka
Karamar hukumar Obingwa
Ciyaman- Dakta Eric Egwuibe
Mataimaki - Mista Chiemela Ekpemu
Ƙaramar hukumar Ugwunagbo
Ciyaman - Kwamared Nosike Ihesiaba
Mataimaki - Mr. Nnamdi Kelvin Chijioke.
Karamar hukumar Ukwa ta gabas
Ciyaman - Dr. Mrs. Ngozi Nwagbara
Mataimaki - Chief Onyebuchi Nnah.
Karamar hukumar Umuahia ta Arewa
Ciyaman - Chief Victor Ikeji
Mataimaki - Mr. Okechukwu Anthony Amah.
Karamar hukumar Aba ta kudu
Ciyaman - MR. Uchechukwu A. C. Wogu
Mafaimaki - Mrs. Nkiru Ugwu.
Karamar hukumar Aba ta arewa
Ciyaman - Ide John Udeagbala
Mataimaki - Prince Nnaemeka Ogbonna
Karamar hukumar Osisioma Ngwa
Ciyaman - Injiniya Israel Nweke
Mataimaki - Barista Young Ngwaziem.
Datti Baba-Ahmed ya yi magana kan hukuncin Kotun koli
A wani rahoton kuma Yayin da Obi ya jaddada cewa yanzu aka fara, abokin takararsa, Datti Baba-Ahmed ya kafe kan cewa ba Tinubu ne ya ci zaɓen 2023 ba.
Ranar Litinin 6 ga watan Nuwamba, Peter Obi ya gudanar da taron manema labarai kan hukuncin Kotun ƙoli da ya tabbatar da nasarar Tinubu.
Asali: Legit.ng