"Ba Zan Taba Daina Kiran Tinubu Dillalin Kwayoyi Ba", Datti Baba Ahmed Ya Bayar da Dalili
- Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Datti Baba-Ahmed ya bayyana dalilin da ya sa ba zai ba Shugaba Tinubu girman da ya kamace shi ba
- A cewar Datti, duk da cewa Tinubu ya girme shi da shekaru amma ba zai iya daina kiran shugaban ƙasan a matsayin dillalin ƙwayoyi ba
- Datti, ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba, yayin da ya dage cewa kotun ƙoli ba ta tabbatar da Tinubu a matsayin shugaban ƙasa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi
FCT, Abuja - Dr. Yusuf Datti Baba-Ahmed, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, ya ce zai mutunta shugaba Bola Ahmed Tinubu ne kawai saboda yawan shekarunsa amma ba zai daina kiransa da dillalin ƙwayoyi ba.
"Kotun ƙoli ba ta tabbatar da nasarar Bola Tinubu a zaɓen 2023 ba" Datti ya faɗi abu 1 da kotun ta yi
Datti Baba-Ahmed yayi magana batun safarar ƙwayoyin Tinubu
Datti Baba-Ahmed ya yi magana ne a ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise, jim kaɗan bayan ya raka Peter Obi, ɗan takarar jam'iyyar LP a zaɓen shugaban ƙasa, zuwa wani taron manema labarai a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A halin da ake ciki dai rahotanni na alaƙanta Shugaba Tinubu da ayyukan da suka shafi safarar muggan kwayoyi shekaru da dama da suka gabata, amma kotun ƙolin da ta yanke hukunci a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba, ta ƙi yanke hukunci kan irin waɗannan batutuwa.
Ku tuna cewa kotun ƙoli a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba ta tabbatar da nasarar da Tinubu ya samu a zaɓen shugaban ƙasa da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
Kotun ƙolin ta tabbatar da hukuncin da kotun zaɓe ta yanke, inda ta yi watsi da ƙararrakin Atiku Abubakar, ɗan takarar jam'iyyar PDP da Obi na LP ke yi kan nasarar Tinubu.
Meyasa Datti ba zai daina kiran Tinubu dillalin ƙwayoyi ba?
Da yake magana kan lamarin, Datti ya dage kan cewa ba zai taɓa girgiza kan wani mutum da ya yi jabun satifiket sannan ya mayar da kuɗaɗen ƙwayoyi, cewar rahoton The Sun.
A kalamansa:
“Ina girmama Tinubu saboda shekarunsa, ya isa ya zama babban yaya na amma hakan ba yana nufin ba zan kira shi dillalin ƙwayoyi ba."
"Ba zan taɓa girgiza da wani mutumin da ya yi jabun satifiket ba, ya mayar da kuɗin ƙwayoyi kuma ya kashe na'urar iREV a lokacin da ya ga muna cin nasara. Ƴan zamba ne, masu cin zarafi ne kuma kowa ya san jam'iyyar Labour ta lashe zaɓen 2023."
Kotun Koli Ba Ta Tabbatar da Nasarar Tinubu ba
A wani labarin kuma, mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Datti Baba-Ahmed ya bayyana cewa kotun ƙoli ba ta tabbatar da Shugaba Tinubu a matsayin shugaban ƙasa ba.
Datti, ya jaddada cewa kotun ƙoli ba ta tabbatar da nasarar Tinubu ba amma ta goyi bayan ƙetare dokar da Kotun zaɓe ta yi.
Asali: Legit.ng