Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Makomar Zaben Sabon Sanatan APC
- Sanata Ifeanyi Ubah ya tabbata kan kujerarsa a matsayin dan majalisar tarayya mai wakiltar Anambra ta kudu
- Kotun daukaka kara da ke zama a Lagas ce ta tabbatar da hakan bayan hukuncin da ta yanke a ranar Juma'a, 3 ga watan Nuwamba
- Kotun ta yi watsi da karar da jam'iyyun adawa uku suka shigar na neman a soke zabensa
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Kotun daukaka kara da ke zama a Lagas, ta tabbatar da nasarar Sanata Patrick Ifeanyi Ubah a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar sanata mai wakiltan Anambra ta kudu a ranar Juma’a, 3 ga watan Nuwamba.
Hakan na zuwa ne bayan sauya shekar sanatan na Anambra ta kudu, wanda a baya yake wakiltar jam'iyyar YPP amma ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki, rahoton Nigerian tribune.
Kotun ta yanke hukunci ne a kan karar da dan takarar jam’iyyar APGA, Hon Chris Azubogu, takwaransa na PDP, Chirs Uba da dan takarar LP, Obinna Uzor suka shigar, Nigerian Tribune ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun daukaka karar ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben yan majalisa da ke Awka, sannan ta yi watsi da karar da yan takarar APGA, PDP da LP suka shigar kan rashin inganci.
Wannan hukunci da kotun daukaka karar ta yanke ya kawo karshen shari’ar zaben kujerar sanatan Anambra ta kudu a zaben 2023.
Kotu ta yanke hukunci a kujerar Goje
A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa kotun daukaka kara a Abuja ta tabbatar da nasarar Danjuma Goje a matsayin sanata mai wakiltan Gombe ta tsakiya.
Kwamitin mutum uku na alkalan kotun sun yi watsi da karar da dan takarar jam'iyyar PDP, Abubakar Aliyu, dangane da zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu, rahoton Daily Trust.
Kotun ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben majalisa a Gombe, wacce a baya ta kori karar da Aliyu da PDP suka shigar kan Goje da jam'iyyar APC. Masu kara dai sun yi zargin cewa an tafka magudi a zaben na 2023.
Asali: Legit.ng