Jam'iyyar LP Ta Tsayar da Dino Melaye Na PDP a Matsayin Dan Takararta a Zaben Gwamnan Kogi
- Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Kogi, Dino Melaye ya yi babban kamu yan kwanaki kafin zaben
- Jam'iyyar LP ta kulla kawance da PDP inda ta lamuncewa Dino a matsayin dan takararta a zaben na ranar 11 ga watan Nuwamba
- A cewar Dino, sun kulla kawancen ne don ceto jihar daga duhu na mulkin APC karkashin jagorancin Yahaya Bello
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Kogi - Jam'iyyar Labour Party ta tsayar da dan takarar jam'iyyar People Democratic Party (PDP) Sanata Dino Melaye a matsayin dan takararta a zaben gwamna da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba, a jihar Kogi.
Melaye ne ya bayyana hakan a ranar Juma'a, 3 ga watan Nuwamba, a wata wallafa da ya yi a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) @_dinomelaye.
Dalilin da yasa LP ta hade da PDP a zaben gwamnan Kogi, Dino Melaye
Tsohon dan majalisar tarayyar ya bayyana cewa an kulla kawancen ne domin tsame jihar Kogi daga duhun gwamnatin APC karkashin jagorancin Gwamna Yahaya Bello.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya rubuta a shafin nasa:
"Ya ku yan jarida, muna farin cikin sanar da ku cewa an kafa tarihi a yau, 4 ga watan Nuwamban 2023. Tarihi ne don ceto jiharmu mai albarka, Kogi da kawar da duhu da ya lullune jiharmu tsaron shekaru bakwai na mulkin APC karkashin jagorancin Alhaji Yahaya Bello.
"A yau, ina sanar da ku wata hadaka tsakanin jam'iyyar People Democratic Party (PDP) da Labour Party(LP) a jihar Kogi don inganta jiharmu. Bayan tattauanawa kuma bisa ra'ayin jiharmu, jam'iyyar LP a wannan rana ta yanke shawarar tsayar da dan takarar gwamnan PDP, Sanata Dino Melaye a matsayin dan takararta a zaben gwamnan jihar Kogi na ranar 11 ga watan Nuwamba.
"Hadin gwiwar don ra'ayin dukkan yan Kogi ne da magoya bayan LP kuma muna umurtan magoya bayanmu a jihar Kogi da su tattara da zaben dan takarar gwamnan PDP, Sanata Dino Melaye a ranar 11 ga watan Nuwamban 2023."
Jiga-jigan PDP sun yi wa Dino kamfen
A wani labarin, mun kawo a baya cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya isa jihar Kogi, tare da gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke da sauran jiga-jigan jam'iyyar PDP.
Saraki da sauransu sun isa Kogi ne don kaddamar da kamfen din jam'iyyar PDP gabannin zaben gwamna na ranar 11 ga watan Nuwamba.
Asali: Legit.ng