Wasu Ministocin Tinubu Mata Suna Shiga Kamar Masu Zuwa Gasar Kyau, Tsohon Ministan Buhari
- Tsohon ministan sadarwa, Adebayo Shittu, ya yi shagube ga wasu ministocin gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu
- Shittu wanda ya yi aiki a gwamnatin Muhammadu Buhari na farko ya ce wasu daga cikin ministocin Tinubu mata suna shiga kamar masu zuwa gasar fidda sarauniyar kyau
- A cewarsa, akwai bukatar ministoci su dunga nuna da gaske aiki ne ya kawo su ba wasa ba
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Adebayo Shittu, tsohon ministan sadarwa, ya ce wasu daga cikin ministocin shugaban kasa Bola Tinubu mata suna shiga sai kace masu zuwa gasar kyau.
Kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto, Shettu ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana a shirin Politics Today na Channels TV a ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamba.
A wajen taron taron kwanaki uku da aka shiryawa Ministoci, hadimai da manyan jami’an gwamanti a ranar Laraba, Tinubu ya yi gargadin cewa za a fatattaki duk ministocin da ba tabuka abun a zo a gani ba daga majalisar tarayya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ministocin Tinubu mata na shiga sai kace za su gasar sarauniyar kyau" - Shittu
Da aka tambaye shi abun da yake ganin ya sa shugaban kasar ya gargadi mambobin majalisarsa, Shettu ya ce:
"Ina farin ciki cewa Shugaban kasa Tinubu ya nada ministoci mata amma a duk lokacin da na gan su a talbijin sai naga kamar suna shirin zuwa gasar kyau ne saboda yanayin shigar da suke sanyawa."
Ya ce akwai bukatar dukkanin ministocin su nuna cewa sun dauki aikin shugabanci ba da wasa ba.
"Ina ganin akwai bukatar mu (APC) a matsayin gwamnati mu nuna jajircewa yayin gudanar da ayyukan da muke da shi a wannan gwamnati," inji shi.
Shittu ya magantu kan tsarin mulkin Tinubu da Buhari
Shittu wanda ya yi aiki a matsayin ministan labarai karkashin gwamnatin tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa 2019, ya kuma kwatanta tsarin shugabancin tsohon ubangidansa da na Tinubu.
Ya ce Buhari bai yi barazanar tsige ministocinsa ba, yana mai cewar tsohon shugaban kasar baya waiwayar wadanda ya bai wa mukami.
Shittu nya ce jan kunnen da Tinubu ya yi wa wadanda ya bai wa mukami yayin taron zai sa su kara zage damtse.
A cewar tsohon ministan, gargadin Tinubu ga ministocin ya nuna cewa yana da niyan yin abubuwan da suka sha banban.
Ya ce Buhari irin shugaban kasar nan ne wanda ke ba wadanda ya nada aiki ba tare da neman jin ya ake ciki ba.
Tinubu na fifita kabilarsa, Farfesa Yusuf
A wani labarin kuma, tsohon babban sakataren hukumar kula da inshoran lafiya, Farfesa Usman Yusuf, ya zargi gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da nuna fifiko wajen rabon mukamai.
Kamar yadda dattijon arewan ya bayyana a cikin wata hira da aka yi da shi, ya ce ana nuna fifiko ga wani bangare na wannan kasar.
Asali: Legit.ng