Tarnaki a NNPP Yayin Da Tsohon Ciyaman Din Jam'iyya Na Kasa Da Dan Takarar Gwamna Suka Koma APC
- Murya ya barke a jam'iyyar APC a yayin da yan jam'iyyun adawa daga NNPP da PDP suka dawo jam'iyyar mai mulki
- Farfesa Rufa'i Ahmed Alkali, tsohon shugaban jam'iyyar NNPP da Sanata Sulaiman Othman Hunkuyi, dan takarar gwamnan NNPP a Kaduna sun shiga APC
- Kazalika, Farfesa Bem Angwe, dan takarar gwamna na NNPP a jihar Benue a zaben 2023 kuma tsohon mai bada shawara kan shari'a a jam'iyyar, shima ya koma APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe
Kaduna - Farfesa Rufai Ahmed Alkali, tsohon shugaban jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), da Sanata Sulaiman Othman Hunkuyi, dan takarar gwamna na NNPP a zaben gwamna na ranar 18 ga watan Maris a jihar Kaduna, sun koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya tarbe su zuwa jam'iyyar a ranar Talata, Daily Trust ta rahoto.
Farfesa Bem Angwe, tsohon mai bada shawara kan shari'a na NNPP kuma dan takarar gwamna a jihar Benue, tare da wasu mutane 23 daga NNPP da PDP suma sun shiga jam'iyyar mai mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganduje ya tarbi tsohon shugaban NNPP na kasa da dan takarar gwamna zuwa APC
Alkali, wanda ya yi magana a madadin wadanda suka sauya shekan, ya ce sun shiga APC ne saboda ita ce jam'iyya mai mulki, ya kara da cewa ita ce jam'iyya mafi dacewa don samun nasara ta siyasa.
Ya ce:
"Yau, mun amince da cewa za mu shiga jam'iyyar APC. A ra'ayin mu, bisa la'akari da yanayin kasar, Mai Girma, Shugaban Kasa Bola Tinubu da sabbin shugabanni karkashin jagorancinka duk gogaggun yan siyasa ne, APC ta canja giya kuma ka bude sabon shafi a tarihin siyasa a kasar nan da ya fi maraba da baki."
Wannan sauya shekar na yan NNPP da PDP shine irinsa na baya-bayan nan a yayin da jam'iyyar mai mulki ke cigaba da karbar masu sauya sheka daga jam'iyyun adawa.
Kwankwaso na shirin sauya tambarin NNPP da gyara dokokin jam'iyya
A wani rahoton kun ji cewa rikicin da ke faruwa a jam'iyyar NNPP ya dauki sabon salo yayin da tsagin Sanata Rabiu Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano ke shirin sauya fasalin jam'yyar.
The Punch ta rahoto cewa tsagin NNPP mai yi wa Kwankwaso biyayya sun fara shirin canja tambarin jam'iyya tare da yi wa kundin tsarin mulki garambawul.
Asali: Legit.ng