Jam'iyyar PDP Ta Shiga Tsakanin Rigimar Gwamna Fubara da Majalisar Dokokin Ribas

Jam'iyyar PDP Ta Shiga Tsakanin Rigimar Gwamna Fubara da Majalisar Dokokin Ribas

  • Jam'iyyar PDP ta sanya baki a rigimar da ta ɓarke tsakanin Gwamnan Fubara da majalisar dokokin jihar Ribas
  • A wata sanarwa da ta wallafa ranar Talata, PDP ta buƙaci masu hannu a rikicin su bada damar yin sulhu don magance matsalar
  • Wannan na zuwa ne yayin da majalisar dokokin ta yi barazanar sauke gwamna Fubara daga kan mulki

FCT Abuja - Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta ƙasa ya fitar da sanarwa kan taƙaddamar da ta ɓarke a jihar Ribas jiya Litinin.

Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa zata shiga tsakani da nufin warware saɓanin da ya shiga tsakanin gwamna Siminalayi Fubara da majalisar dokokin jihar Ribas.

Gwamnan jihar Ribas, Similanayi Fubara.
Jam'iyyar PDP Ta Tsoma Baki Kan Rikicin Gwamna da Majalisar Dokokin Ribas Hoto: Sir Similanayi Fubara
Asali: Facebook

Idan baku manta ba mun kawo muku rahoton cewa Fubara ya sha hayaki mai sa hawaye a kan hanyar sa ta zuwa zauren majalisar a ranar Litinin, 30 ga watan Oktoba, 2023.

Kara karanta wannan

Fubara da Ministan Abuja sun haɗu a Aso Villa ana ƙishin-kishin ɗin Tsige Gwamnan PDP

Hakan ya biyo bayan yunkurin tsige gwamnan daga mulki wanda majalisar dokokin ta fara ranar Litinin, kuma ta sanar da shi matakin da take shirin ɗauka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da haka Gwamnan ya ƙarisa zauren Majalisar, inda ya ce babu wata hujja a kan batun tsige shi, ya kuma yi Allah wadai da ayyukan ‘yan sandan da ya ce sun harbe shi kai tsaye.

PDP ta tsoma baki

Jam'iyyar PDP ta maida martani kan wannan rigima a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na manhajar X watau Tuwita ranar Talata, 31 ga watan Oktoba, 2023.

Sanarwan ta ce:

"Kwamitin NWC na jam’iyyar PDP na kira ga duk masu hannu a rikicin da ke faruwa a jihar Ribas da su maida takubbansu kube, su bada damar yin sulhu cikin lumana da kwanciyar hankali."
“NWC ya bukaci dukkan mambobin PDP da magoya baya su kwantar da hankali tare da tabbatar da cewa ta fara aikin warware saɓani da rashin jituwar da ke faruwa."

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Manyan abubuwa 2 da suka haddasa rigima tsakanin Wike da Gwamna Fubara

"Muna kira ga dukkan shugabanni, masu ruwa da tsaki da kuma ‘ya’yan PDP a Ribas da su hada kai, su maida hankali kan babban aikin gudanar da mulki da samar da romon dimokuradiyya ga al'umma."

Fubara da Ministan Abuja sun haɗu a Aso Villa

A wani rahoton kuma Gwamna Fubara da Ministan Abuja, Nyesom Wike sun gana a Villa yayin da ake ƙishin-ƙishin ɗin tsige gwamnan na jihar Ribas.

Manyan kusoshin jam'iyyar PDP biyu sun haɗu, inda suka gaisa cikin farin ciki yayin taron majalisar gudanarwa ta ƴan sanda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262