Fubara da Ministan Abuja Sun Haɗu a Aso Villa Ana Tsaka da Shirin Tsige Gwamnan PDP
- Gwamna Fubara da Ministan Abuja, Nyesom Wike sun gana a Villa yayin da ake ƙishin-ƙishin ɗin tsige gwamnan na jihar Ribas
- Manyan kusoshin jam'iyyar PDP biyu sun haɗu, inda suka gaisa cikin farin ciki yayin taron majalisar gudanarwa ta ƴan sanda
- Duk da babu bayanin abin da suka tattauna a lokacin amma ana fatan hakan zai kawo karshen rigimar da ta haɗo su
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, sun haɗu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja yau Talata.
Channels tv ta tattaro cewa an ga jiga-jigan siyasar guda biyu sun yi musabaha da juna yayin da suka haɗu.
Wannan haɗuwa ta gwamnan da magabacinsa, mambobin jam'iyyar PDP, ya biyo bayan yunƙurin da majalisar dokokin jihar Ribas ta fara na sauke gwamna Fubara daga mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meya haɗa Wike da Fubara a Villa?
An tattaro cewa Fubara da tsohon gwamnan jihar Ribas da ya sauka, Wike sun je fadar shugaban ƙasa ne domin halartar taron majalisar gudanarwa ta hukumar yan sandan Najeriya.
Wannan majalisa dai ita ke da alhakin sanya ido da tafiyar harkokin rundunar ƴan sandan ƙasar nan daidai da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, shi ke jagorantar wannan majalisa kuma ta ƙunshi gwamnonin jihohin ƙasar nan baki ɗaya, shugaban hukumar jin daɗin 'yan sanda da IGP.
Taro na ƙarshe da majalisar ta gudanar shi ne wanda aka yi ranar 4 ga watan Yuni, 2023, wanda shugaban ƙasa a wancan lokacin, Muhammadu Buhari, ya jagoranta.
Me suka tattauna a taron?
Har kawo yanzu da muke haɗa muku wannan rahoton ba a bayyana ainihin abin da manyan ƙusoshin suka tattauna ba, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Sai dai ana tsammanin wannan zama na su zai haifar da sakamako mai kyau wanda zai warware saɓanin da ya shiga tsakaninsu.
Tinubu ya aika saƙo zuwa majalisa
A wani rahoton kuma Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu , ya rubuta wasiƙa zuwa majalisar wakilan tarayya kan sabon ƙarin kasafin kuɗi na shekarar 2023.
Ya yi bayanin cewa a za a yi amfani da wannan ƙarin kasafin wajen cike gurbin ƙarin albashin da aka yi wa ma'aikatan tarayya, tsaro da sauransu.
Asali: Legit.ng