Jam'iyyar PDP Ta Maida Martani Kan Rashin Nasarar Atiku a Kotun Koli

Jam'iyyar PDP Ta Maida Martani Kan Rashin Nasarar Atiku a Kotun Koli

  • Babbar jam'iyyar adawa PDP ta nuna tsananin takaicinta bisa kayen da ta sake sha a Kotun ƙolin Najeriya
  • Kotun da ake wa taken daga ita sai Allah ya isa ta tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasan 2023
  • Bayan haka ne, jam'iyyar PDP ta bayyana cewa tsarin zaɓen Najeriya ba mai kyau bane kuma zata yi duk mai yiwuwa wajen ganin an gyara

FCT Abuja - Jam’iyyar PDP ta ce ta kadu matuka da hukuncin da kotun koli ta yanke kan karar da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar ya shigar.

Idan baku manta ba, Atiku, tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya kalubalanci nasarar shugaba Tinubu a zaben da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Shugaba Tinubu da Atiku.
Jam'iyyar PDP Ta Maida Martani Kan Rashin Nasarar Atiku a Kotun Koli Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

PDP ta maida martani

A wata sanarwa da Legit Hausa ta gani mai ɗauke da sa hannun sakataren watsa labarai, Debo Ologunagba, jam'iyyar PDP ta ce Kotun ƙoli ta bai wa 'yan Najeriya kunya.

Kara karanta wannan

Bayan Atiku Ya Sha Kaye a Kotun Ƙoli, Shugaban Matasan PDP Ya Shiga Babbar Matsala

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta kuma jaddada aniyarta da cewa zata tsaya tsayin daka wajen ganin an samar da, "Ingantaccen tsarin zaɓe wanda zai iya kawo gwamnatin da mutane suka zaɓa."

Wani sashin sanarwan da PDP ta fitar ya ce:

"PDP da mafi akasarin 'yan Najeriya sun kaɗu kuma sun ji takaici matuka tare da damuwa bisa hukuncin da kotun ƙoli ta yanke. PDP na gankn hakan ba zai haifar da ɗa mai ido ba."
“PDP ta tabbatar da cewa, hakika wannan abu ne mai ban tausayi ga dimokuradiyyar ƙasar nan ganin cewa Kotun Koli ta kasa tabbatar da tanade-tanaden doka."
"Maimakon haka, ta yi watsi da tsammanin mafi yawan ‘yan Najeriya da ke kallonta a matsayin mafakar da da zasu kwato haƙƙinsu."

Jam'iyyar PDP ta kara da cewa har yanzu tana zargin APC mai mulki da hannu a tafka kura-kurai da maguɗi a zaben da ya gabata.

Kara karanta wannan

Abun Mamaki: Gwamnan PDP Ya Je Villa Tare da Ƙusoshin APC, Ya Taya Tinubu Murnar Nasara a Kotu

A cewarta, wannan hukuncin ya rage yarda da ƙarfin ƙwarin guiwar da yan Najeriya ke da su kan cewa zasu samu adalci a ɓangaren shari'a.

Gwamnan PDP ya taya Tinubu murna

A wani rahoton kuma yayin da ake tsaka da murnar nasarar shugaba Tinubu a Kotun ƙoli, Gwamnan PDP ya je fadar shugaban ƙasa ya taya shi murna.

A wani faifan bidiyo da ke yawo, an ga gwamna Diri ya taka har zuwa wurin da Tinubu ke tsaye, ya miƙa masa hannu suka gaisa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262