Hukuncin Kotu: Gwamnan PDP Ya Garzaya Ofishin Tinubu Tare da Jiga-Jigan APC

Hukuncin Kotu: Gwamnan PDP Ya Garzaya Ofishin Tinubu Tare da Jiga-Jigan APC

  • Yayin da ake murnar nasarar shugaba Tinubu a Kotun ƙoli, Gwamnan PDP ya je fadar shugaban ƙasa ya taya shi murna
  • A wani faifan bidiyo da ke yawo, an ga gwamna Diri ya taka har zuwa wurin da Tinubu ke tsaye, ya miƙa masa hannu suka gaisa
  • A ɗazu ne Ƙotun koli ta tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu bayan ta kori kararrakin Atiku da Peter Obi

FCT Abuja - Ɗaya daga cikin gwamnonin PDP ya garzaya fadar shugaban ƙasa da ke Abuja inda ya taya shugaba Bola Ahmed Tinubu murnar samun nasara a Kotun Ƙoli.

Wannan na zuwa ne bayan Kotun ƙolin Najeriya ta tabbatar da nasarar shugaban ƙasa Bola Tinubu a zaben da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a Villa.
Hukuncin Kotu: Gwamnan PDP Ya Garzaya Ofishin Tinubu Tare da Jiga-Jigan APC Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Manyan abokan hamayyar Tinubu a zaben da ya wuce, Alhaji Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP ne suka ƙaubalanci nasarar APC a Kotun, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

"Abun Takaici"Jam'iyyar PDP Ta Maida Zazzafan Martani Kan Rashin Nasarar Atiku a Kotun Ƙoli

A hukuncin da aka yanke aranar Alhamis, kwamitin alƙalai bakwai ya ce batutuwan da Obi ya zayyana iri daya ne da na Atiku don haka babu bukatar a maimaita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Saboda haka ta ƙara tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa, wanda ta tabbatar da nasarar Tinubu a zaben da ya shuɗe, im ji Premium Times.

Jiga-jigai sun cika Villa don taya murna

Bayan yanke wannan hukunci ne, manyan ƙusoshi da masu fatan alheri suka durfafi fadar shugaban ƙasa domin taya Bola Tinubu murnar nasarar da ya samu.

Ana cikin haka ne kwatsam aka hangi gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, mamban jam'iyyar PDP a wani faifan bidiyo yana taya shugaba Tinubu murna.

An ga gwamna Diri ya taka har zuwa wurin da shugaba Tinubu yake kuma ga miƙa masa hannu suka yi musabaha.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Ƙasa Buhari Ya Maida Martani Mai Jan Hankali Kan Hukuncin Kotun Ƙoli

Tinubu da ke ta murna sai aka ji yana cewa, "Oh! Diri, kana da kyau fa. Na kan gan shi a talabijin.”

Haka nan kuma an ga Nyesom Wike, Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) Abuja, wanda kuma jigo ne a jam’iyyar PDP a ofishin shugaban kasa.

Gwamna Diri na kokarin ta zarce kan kujerarsa a zaben jihar Bayelsa nan da 'yan makonni yayin da babban abokin adawarsa na APC, Timipre Sylva, kotu ta soke takararsa.

Buhari Ya Taya Shugaba Tinubu Murna

A wani rahoton kuma Muhammadu Buhari ya yi maraba da hukuncin Kotun ƙoli wanda ya tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023.

Tsohon shugaban ya ce matakin da Kotu mai daraja ta ɗaya ta ɗauka abu ne mai kyau da zai kawo natsuwa bayan tsawon lokaci ana shari'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262