Muhammadu Buhari Ya Taya Shugaba Tinubu Murna, Ya Yaba da Hukuncin Kotun Koli

Muhammadu Buhari Ya Taya Shugaba Tinubu Murna, Ya Yaba da Hukuncin Kotun Koli

  • Muhammadu Buhari ya yi maraba da hukuncin Kotun ƙoli wanda ya tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023
  • Tsohon shugaban ya ce matakin da Kotu mai daraja ta ɗaya ta ɗauka abu ne mai kyau da zai kawo natsuwa bayan tsawon lokaci ana shari'a
  • Ya yi kira yan adawa da su kama hannun abota wanda gwamnatin Tinubu da Shettima ta miƙo musu tun da farko

FCT Abuja - Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya taya shugaba Bola Ahmed Tinubu murna bisa nasarar da ya samu a Kotun kolin Najeriya.

Buhari ya kuma yi wa magajinsa da sauran muƙarrabansa fatan samun nasara a zangon mulkinsu na farko, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Buhari ya taya Bola Tinubu murna.
Muhammadu Buhari Ya Taya Shugaba Tinubu Murna, Ya Yaba da Hukuncin Kotun Koli Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: UGC

Tsohon shugaban ya ayyana hukuncin da Kotun ƙoli ta yanke na korar ƙorafe-ƙorafen Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP a matsayin abin farin ciki da nutsuwa gare shi da sauran 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

"Abun Takaici"Jam'iyyar PDP Ta Maida Zazzafan Martani Kan Rashin Nasarar Atiku a Kotun Ƙoli

Muhammadu Buhari ya faɗi haka ne a wata sanarwa da tsohon mai magana da yawun shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Alhamis, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da Buhari ya faɗa kan hukuncin Kotu

Ya nanata abinda ya faɗa a lokacin da Kotun sauraron ƙararrakin zabe ta yanke hukuncin tabbatar da nasarar Tinubu, inda ya ce hukuncin ya ƙara, "tabbatar da muradin mafi akasarin 'yan Najeriya.

Buhari ya ƙara da cewa, "A yanzu mun kawo gabar ƙarshe bayan shafe watanni takwas ana fafata shari'a mai wahala, ya kamata ƙasar nan ta sarara ta samu hutu."

"Yan adawa sun yi faɗa mai tsafta, amma tun da sun gama amfani damar da kundin tsarin mulki ya ba su, ina ga ya kamata su kama hannun abotan da gwamnatin Tinubu/Shettima ta miƙo musu."

Kara karanta wannan

Abun Mamaki: Gwamnan PDP Ya Je Villa Tare da Ƙusoshin APC, Ya Taya Tinubu Murnar Nasara a Kotu

"Su kyale gwamnati ta maida hankali kan mulki ta yadda mutane zasu sha romon alkawurran da jam'iyyar APC ta ɗaukar masu."

Daga ƙarshe, Muhammadu Buhari ya nuna damuwarsa kan karancin masu fitowa su kaɗa kur'a lokacin zaɓe musamman a birane, yana mai cewa ya kamata a samu sauyi.

Ya kamata mu haɗa kai - Barau

A wani rahoton kuma Sanata Barau Jibrin ya jinjina wa Alkalan Kotun ƙoli bisa hukuncin da suka yanke na tabbatar nasarar Bola Tinubu a zaɓen 2023.

Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya roƙi masu kara, Atiku da Obi, su haɗa hannu da Tinubu don ci gaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262