CJN Ariwoola Ya Amince a Haska Hukuncin Kotun Koli Kai Tsaye

CJN Ariwoola Ya Amince a Haska Hukuncin Kotun Koli Kai Tsaye

  • Kamar yadda aka yi a kotun sauraran zabe, za a haska shari'ar kotun koli na karshe kan shari'arsu Atiku, Obi da Tinubu a gidajen talabijin
  • Hakan na nufin yan Najeriya na gida da waje, za su iya saka ido kan yadda shari'ar ke gudana daga gidajensu da wuraren aiki
  • Alkalin alkalan Najeriya, CJN, Olukayode Ariwoola, ya amince a haska shari'ar kai tsaye a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba

Ma'aikacin jaridar Legit Hausa Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

FCT, Abuja - Alkalin Alkalan Najeriya, Olukayode Ariwoola, ya amince a haska shari'ar Kotun Kolin kan shari'an daukaka kara kan zaben shugaban kasa na 2023.

An tabbatar da hakan ne a ranar Alhamis, 26 ga watan Okotoban shekarar 2023.

Kara karanta wannan

"Peter Obi Ba Zai Taba Zama Shugaban Kasar Najeriya Ba": Inji Reno Omokri Bayan Hukuncin Kotun Koli

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ikirarin rashin cancantar Tinubu

A ranar Litinin, 23 ga watan Oktoba, babban kotun kasar ta fara duba daukaka karar da yan takarar jam'iyyun adawa suka shigar na neman soke nasarar Tinubu da ya samu a zaben watan Fabrairu.

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar da Peter Obi na jam'iyyar Labour, LP, ne suke kallubalantar nasarar na Tinubu.

Yan takarar na jam'iyyun adawa sun nuna damuwa kan cancantar Shugaba Tinubu da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima. Babban batun da ake zargi shine an zabi Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa da kuma sanata duk lokaci guda.

A watan Yunin 2022, Tinubu, yayin mika fom dinsa na takarar shugaban kasa ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC, ya zabi Ibrahim Masari, dan siyasa daga Katsina a matsayin 'dan rikon kwarya'.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kotun Koli Ta Tabbatar Da Tinubu a Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa Na 2023

Kashi 25 a Abuja

Wani babban batu da ake tattaunawa shine lauyoyin Peter Obi, wanda suka ce Tinubu bai ci kuri'u kashi 25% ba a Abuja, wanda a cewar jam'iyyar adawar, na nufin bai cika ka'idar a ayyana shi matsayin shugaban kasa ba.

A cewar dokar zaben Najeriya, dan takara zai zama shugaban kasa ne bayan ya samu a kalla kashi 25 na kuri'u a kashi biyu cikin uku na jihohi 36 na kasa da Abuja.

Akasin haka, Tinubu ya ce kashi 25 din da ake nufi ya shine idan an gwamutsa dukkan jihohin da Abuja.

Wasu abubuwa da kotun za ta yanke hukunci a kai sun hada da gazawar INEC na nuna sakamakon zabe kai tsaye da takardun karatun Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164