NNPP Ta Arewa Maso Yamma Ta Goyi Bayan Korar Kwankwaso Daga Jam'iyyar
- Sanata Rabiu Kwankwaso ya sake shiga matsala a jam'iyyar NNPP yayin da masu ruwa da tsakin Arewa maso Yamma suka juya masa baya
- A wani taro da suka gudanar, jiga-jigan NNPP sun amince da matakin da aka ɗauka na korar Kwankwaso daga jam'iyyar
- Sun kuma bayyana cewa suna goyon bayan jagorancin shugaban jam'iyyar NNPP na ƙasa, Mejo Agbor
Jiga-jigan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar NNPP reshen Arewa maso Yamma sun amince da matakin korar tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, daga jam'iyyar.
Masu ruwa da tsakin sun bayyana goyon bayansu ga matakin korar Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 a inuwar NNPP daga cikin jam'iyyar.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da shugaban NNPP na shiyyar Arewa Maso Yamma, Alhaji Sani Yusuf, ya fitar kan batun.
"A Hankali Mu Na Rikidewa Zuwa Lalatacciyar Jam'iyar PDP", Jigon APC Ya Soki Tsarin Shugabancin Jam'iyyar
Ya ce a wani taron masu ruwa da tsaki da suka gudanar, sun cimma matsayar goyon bayan matakin da kwamitin amintattu (BoT) da kwamitin gudanarwa (NWC) suka ɗauka kan Kwankwaso.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, korar da aka yi wa Kwankwaso, "tare da sauran masu taimaka masa wanda BoT da NWC suka yi ya zo daidai da ra'ayin masu ruwa da tsakin shiyyar."
Taron ya kuma bukaci a sake dawo da shugabannin kwamitocin gudanarwa na jam'iyyar a jihohi 10 waɗanda NWC da aka rushe ƙarƙashin Ali Kawo ya kora.
A cewar masu ruwa da tsakin Arewa maso Yamma, maida shugabannin kan muƙamansu zai zama wata hanya mai kyau ta sasanta rikicin da ke faruwa a NNPP.
Sun amaince da shugabancin Agbor
Bayan haka, masu ruwa da tsakin sun kaɗa kuri'ar kwarin guiwa da mubaya'a ga jagorancin shugaban NNPP na ƙasa, Mista Mejo Agbor, Channels tv ta ruwaito.
Sanarwar ta umarci masu ruwa da tsaki da su ƙara jajircewa kuma su fara jawo hankalin ‘yan Najeriya domin yin rijista da NNPP da nufin shirya zuwan zabe na gaba.
Shugaba Tinubu Ya Ƙara Yin Gyara
Kuna da labarin Bola Ahmed Tinubu ya ɗauko gogaggen injiniya ya naɗa shi a matsayin sabon shugaban hukumar makamashi ta Najeriya (ECN).
A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun kakakin shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, Tinubu ya naɗa Dokta Abdullahi Mustapha ya jagoranci ECN.
Asali: Legit.ng