Kotun Koli Ta Hango Kuskure a Wasikun Jami'ar CSU Kan Takardun Tinubu

Kotun Koli Ta Hango Kuskure a Wasikun Jami'ar CSU Kan Takardun Tinubu

  • Kotun koli ta saurari ƙarar da Atiku Abubakar ya shigar, dangane da sahihancin takardar shaidar Bola Tinubu da ya samu daga jami’ar jihar Chicago.
  • Atiku na jam'iyyar PDP na zargin cewa shugaban ƙasar ya gabatar da takardun jabu na jami'ar jihar Chicago
  • Da yake magana kan ƙarar a ranar Litinin, mai shari’a Okoro ya koka kan wasiƙun da CSU ta bayar kan takardar shaidar Tinubu

FCT, Abuja - Kotun ƙoli a ranar Litinin, 23 ga watan Oktoba, ta bayyana cewa akwai wasiƙu masu karo da juna daga jami'ar jihar Chicago (CSU) kan takardar shaidar karatun Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Mai shari’a John Okoro, jagoran kotun mai alƙalai mutum bakwai da ke sauraron buƙatar da Atiku Abubakar, ɗan takarar jam'iyyar PDP, ya shigar kan nasarar da Tinubu ya samu, shi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, 23 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Wasu Ministoci da Jiga-Jigan FG a Villa, Bayanai Sun Fito

Kotun koli ta yi magana kan wasikun CSU
Kotun koli ta yi magana kan wasikun da jami'ar CSU ta bayar kan takardun Tinubu Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Kotu ta hango ruɗani a wasiƙun jami'ar CSU

Da yake jawabi a zaman kotun, Mai shari’a Okoro, ya ce dole ne a tabbatar da abubuwan da suka shafi laifuka ba tare da wata shakka ba, a cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Amma a wannan yanayin, akwai wasiƙu guda biyu masu cin karo da juna daga CSU, ɗaya na tabbatar da takardar shaidar karatun shugaban ƙasa, ɗaya kuma ta bayyana rashin sahihancinsa. Da wanne zamu dogara?” Ya tambaya.

Kotun koli ta yi watsi da ƙarar da APM ta ɗaukaka

Kotun ƙoli ta yi watsi da ƙarar da jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM) ta shigar.

Ƙarar dai tana ƙalubalantar zaɓen Kashim Shettima a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar APC.

Kotun da Okoro yake jagoranta ta yi watsi da ƙarar bayan lauyan wanda ya shigar da kara, Chukwuma Majukwu Umeh, ya nemi janye ƙarar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun Koli Ta Dage Sauraron Daukaka Karar Atiku, Peter Obi, Ta Yi Watsi da Karar APM

Alkalan da Za Su Saurari Daukaka Kara

A wani labarin kuma, kotun ƙoli ta bayyana alƙalai bakwai waɗanda za su saurari ɗaukaka ƙarar da aka yi kan nasarar Shugaba Tinubu a zaɓen 2023.

Kotun ƙolin ta sanar da cewa Uwani Musa Abba Aji, Helen Morenkeji Ogunwumiju su ne mata biyu da ke cikin alƙalan bakwai da za su saurari ƙarar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel