Gwamnan Kano: Ayodele Ya Yi Hasashen Yadda Za Ta Kaya Tsakanin NNPP Da APC a Kotun Koli
- Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano ta tsige Gwamna Abba Yusuf a watan Satumba
- Gwamna Yusuf ya kasance jigon jam'iyyar NNPP kuma yaron tsohon gwamnan jihar, Rabi'u Kwankwaso a siyasa
- Kotun zaben ta ayyana dan takarar jam'iyyar APC, Nasiru Gawuna, a matsayin wanda ya lashe zaben
Jihar Kano - Babban malamin addini a Najeriya, Primate Babatunde Elijah Ayodele, ya yi hasashen cewa jam'iyyar APC ce za ta sake samun nasara idan jam'iyyar NNPP ta daukaka kara kan hukuncin tsige Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar Kano.
Ayodele ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, 18 ga watan Oktoba. Legit Hausa ce ta gano bidiyon.
"Kano za ta zama ta APC": Ayodele
Malamin addinin ya ce idan har alkalan ba su yi magudi ba, APC za ta sake kayar da NNPP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalamansa:
“Kano, Kano za ta koma ga APC. NNPP ko ma me kike, kina bacci. Wannan yana da tsanani. Cewa APC za ta yi maki harbi daya ne, kuma shikenan.
"Kuma koma menene, APC ce za ta yi nasara a kotun koli, sai dai idan alkalan sun yi murdiya. Wannan shine kawai abun da ke ciki."
Ku tuna cewa yayin da kotun zaben gwamnan Kano ta ayyana Nasiru Gawuna na APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna na ranar 18 ga watan Maris, Yusuf, dan takarar NNPP a zaben ya yi ikirarin cewa hukuncin ya keta haddin doka.
Jam'iyyar ta NNPP ta sha alwashin kalubalantar hukuncin kotun zaben saboda kundin tsarin mulkin Najeriya ta ba mai kara damar daukaka kara a kotun daukaka kara da kotun koli."
Yan jam’iyyar APC a Kano sun koka kan yadda Abba Gida Gida ya nuna wariya a rabon kayan tallafi
A wani labari na daban, mun ji cewa ‘Yan jam’iyyar APC a jihar Kano sun koka kan yadda gwamnatin jihar ta nuna wariya kan rabon kayan abinci na tallafi.
A makon da ya gabata ne Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da rabon kayan tallafin abinci na masara da shinkafa na tallafi da Gwamnatin Tarayya ta bayar.
Asali: Legit.ng