"Abin da Ya Sa Ya Fice Daga Zauren Majalisa Bayan Akpabio Ya Katse Ni" Ndume

"Abin da Ya Sa Ya Fice Daga Zauren Majalisa Bayan Akpabio Ya Katse Ni" Ndume

  • Sanata Ali Ndume ya bayyana asalin dalilin da ya sa aka ga ya fice daga zauren majalisar dattawa ana tsaka da zama ranar Talata
  • Rahoto ya nuna cewa Ndume ya tattara kayansa ya bar zauren bayan Sanata Akpabio ya hana shi damar yin magana
  • Ya ce lamarin ya faru ne a daidai lokacin Sallah shiyasa ya fita amma aka fassara fitarsa da wata ma'ana ta daban

FCT Abuja - Mai tsawatarwa na majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ali Ndume, ya yi bayani kan asalin dalilin da ya sa ya fice daga zauren majalisa ana tsaka da zama ranar Talata.

Idan baku manta ba mun kawo muku rahoton cewa Ndume ya fita daga majalisar a fusace bayan ya takali shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.

Sanata Ali Ndume.
Sanata Ndume ya bayyana abin da ya sa ya fice daga zauren majalisa Hoto: Ali Ndume
Asali: Facebook

Sanata Ndume daga jihar Borno ya kalubalanci Akpabio kan yadda yake tafiyar da harkokin majalisar wanda a tunaninsa ya saɓa wa doka da ka'idoji.

Kara karanta wannan

Yaki Da Rashawa: Ka Da Ka Yi Misali Da Ni, Akpabio Ya Fada Wa Shugaban EFCC

Yana cikin jawo hankali ne Akpabio ya katse shi ya hana shi ƙarisa jawabin da ya ɗauko, lamarin da ya tunzura shi ya bar zauren majalisar, Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asalin abin da ya faru tun da farko - Ndume

A wata hira da BBC Hausa, Ndume ya bayyana dalilinsa na ficewa daga zauren majalisar dattawa lokacin da ake ta muhawara kan batun rufe iyakokin Najeriya.

Ya bayyana cewa lamarin ya samo asali ne daga “lokacin da Sanata Kawu Sumaila ya gabatar da kudirin da ya ce na gaggawa ne kan rufe iyakar Najeriya da Nijar."

“Da farko an yi jayayya cewa kudirin ba na gaggawa ba ne, amma shugaban majalisar dattawa ya kyale shi ya karasa abin da yake son fada."
“Bayan sauraron kudirin, kowa ya amince da cewa tunda yana da alaka da tsaro ya kamata a ɗan dakatar da shi.”

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Ya Soki Amurka a Kan Goyon Bayan Israila Wajen Hallaka ‘Yan Gaza

A cewarsa, a lokacin ne ya so bayyana wa zauren majalisar mahimmancin kudirin, amma shugaban majalisar dattawan ya hana shi damar yin magana.

“Ba shugaban Najeriya ne ya rufe iyakokin ba, sai dai a lokacin da yake a matsayin shugaban kungiyar ECOWAS. Don haka, yana da ikon kai ƙorafin mu."
Ana cikin haka sai ya zo daidai da lokacin sallah, wanda ya sa na tashi na fito, abokan aikina sun yi kuskuren fahimtar fitowata, su kuma ’yan jarida sun canza ma’anar fitowata."

- In ji Ali Ndume.

Ya ƙara da cewa ya faɗa wa mataimakinsa cewa zai tafi ya yi sallah, sannan ya fito daga zauren.

Majalisar Dattawa Ta Bi Umarnin Tinubu, Ta Tabbatar a Nadin Manyan Mukaman da Ya Tura

A wani rahoton kuma Majalisar Dattawa a yau ta tabbatar da sabbin mukamai uku da Shugaba Tinubu ya tura musu don tantancewa.

Majalisar ta tabbatar da Ola Olukoyede a matsayin shugaban Hukumar EFCC da sakatarensa, Mohammed Hammajoda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262