Lucky Aiyedatiwa: Yan Majalisar Dokokin Jihar Ondo Sun Dakatar da Shirin Tsige Mataimakin Gwamna
- Ƴan majalisar dokokin jihar Ondo sun dakatar da shirinsu na tsige mataimakin gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa
- Ƴan majalisar dokokin sun cimma wannan matsayar ne bayan sun gana da shugaban APC na ƙasa da kwamitin sulhu
- An yi ta kai ruwa rana dai kan batun tsige mataimakin gwamnan tun bayan da gwamna Akeredolu ya dawo daga jinya
FCT, Abuja - Ƴan majalisar dokokin jihar Ondo, a jiya Talata, 17 ga watan Oktoban 2023, sun gana da kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ƙarƙashin jagorancin Dr Abdullahi Ganduje.
Ƴan majalisar sun cimma matsayar dakatar da shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Ondo, Lucky Ayedatiwa, cewar rahoton Vanguard.
Ayedatiwa dai ya kasance yana fuskantar bincike tare da barazanar tsige shi daga muƙaminsa bisa zarginsa da aikata ba daidai ba.
Yanzu-Yanzu: Gwamna Zulum Ya Bayar da Muhimmin Umarni Bayan Miyagu Sun Halaka Diyar Dan Majalisa a Jihar Borno
Meyasa aka dakatar da shirin tsige shi?
Daily Trust ta ce da yake jawabi bayan wata ganawar sirri da aka shafe kimanin sa’o’i biyu ana yi a sakatariyar jam’iyyar APC ta ƙasa da ke Abuja, Ganduje da kakakin majalisar, Mista Oladeji Olamide sun tabbatar da dakatar da shirin tsige shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron na ranar Talata ya samu halartar mambobin NWC na jam'iyyar, kwamitin sulhu na mutane 9 ƙarƙashin Aminu Bello Masari, da shugaban jam’iyyar na jiha, Ade Adetimehin da 18 daga cikin 22 na ƴan majaisar dokokin jihar ƙarƙashin jagorancin kakakin majalisar Olamide.
Shugaban kwamitin sulhu kuma tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana cewa:
"A yanzu haka an dakatar da bincike da tsige shi domin bai wa kwamitin damar yin aiki. Mun gana da duk masu ruwa da tsaki, sai dai gwamnan da muke cigaba da ƙoƙarin ganin mun gani.
Ƴan majalisar za su ba APC haɗin kai
Da yake tabbatar da cewa ƴan majalisar sun je Abuja ne bisa buƙatar shugaban jam'iyyar na ƙasa da kwamitin sulhu, kakakin majalisar ya ce ƴan majalisar a shirye suke su ba jam'iyyar haɗin kai.
A kalamansa:
“Mun yi alkawarin yin aiki tare da shugaban jam'iyya da kuma shugaban kwamitin sulhu domim ganin an magance rikicin siyasa a jihar Ondo."
"Mun yi alƙawarin cewa a namu bangaren, a shirye muke mu ba jam'iyyar hadin kai a matsayin ɓangaren gwamnati. Haka kuma, a duk lokacin da suke son ganawa da mu, za mu amsa gayyata. Mafi mahimmanci, za mu ƙyale kwamitin su yi aikinsu ba tare da kawo cikas ba."
Gwamnatin Ondo Ta Magantu Ƙan Sake Fitar da Akeredolu
A wani labarin kuma, gwamnatin jihar Ondo ta musanta batun cewa ana shirin sake fitar da gwamna Akeredolu domin yin jinya a ƙasar waje.
Gwamnatin ta bayyana cewa rahotannin da ake yaɗawa kan sake fitar da gwamnan ba su da tushe ballantana makama.
Asali: Legit.ng