"Yarbawa Kirista Ake Fifitawa": MURIC Ta Soke Tinubu Kan Nade-Nade

"Yarbawa Kirista Ake Fifitawa": MURIC Ta Soke Tinubu Kan Nade-Nade

Ikeja, Legas - Kungiyar kare hakkin musulmi a Najeriya mai suna Muslim Rights Council (MURIC), ta yi korafi kan nade-naden da Shugaba Bola Tinubu ke yi a yankin Kudu maso Yammacin kasar a baya-bayan nan.

Kungiyar ta bayyana nade-naden a matsayin 'Kirista da Kirista a tikitin Musulmi da Musulmi".

MURIC ta zargi Tinubu da fifita yarbawa kiristoci wurin nadin mukami
MURIC ta ce ba ta jin dadin nade-naden Shugaba Tinubu. Hoto: Dr AbdulHakeem AbdulLateef, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

"Babban Hafsan Soja, COAS Taoreed Lagbaja Kirista ne", MURIC ta yi ikirari

Hakan na dauke cikin sanarwa da shugaban kungiyar Farfesa Ishaq Akintola ya fitar a ranar Talata, 17 ga watan Oktoba. Legit Hausa ta samu sanarwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesa Akintola ya ce:

"Ya zama dole mu sake bayyana fargabar da musulmin Najeriya ke da shi game da nade-naden da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi a yankin Kudu maso Yamma a baya-bayan nan. Musulmi masu sanya idanu kan lamura da masu fashin baki sun yarda cewa nade-naden ya fi karkata ga Yarbawa Kirista.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Ya Soki Amurka a Kan Goyon Bayan Israila Wajen Hallaka ‘Yan Gaza

"Daga cikin manyan mukaman da aka bai wa Yarbawa kirista sun hada da shugabannin Hukumar Tura Sakonni, NIPOST, Shugaban Hukumar Kare Bayannan Sirri, NDPC, Shugaban Hukumar Kula Da Shaidar Zama Dan Kasa, NIMC, Shugaban Hukumar Tattara Haraji na Kasa, Sufeta Janar na Yan Sanda, Ministan Kudi da Gwamnan Babban Bankin Najeriya.
"Majiyoyi da ba a tantance sahihancinsu ba sun yi ikirarin cewa Babban Hafsan Sojojin Najeriya shima kirista ne duk da yana da suna na musulmi.
"7 cikin ministocin Kudu maso Yamma kirista ne. Shugaban kwamitin yi wa tsarin karbar haraji garambawul da mashawarci na musamman kan harkokin tattalin arziki, duk kiristoci ne Yarbawa. Mashawarta na musamman da manyan mashawarta, da hadimai na musamman daga Kudu maso Yamma duk kirista ne suma."

Bugu da kari, MURIC ta ce wannan lamarin abin tambaya ne. Kungiyar kuma ta yi ikirarin cewa an mayar da musulmi saniyar ware a gwamnatin Tinubu.

MURIC Ta Jinjinawa Abba Kabir Yusuf Kan Haramta Amfani Da Wasu Littafai a Kano

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Nada Matashiya Yar Shekaru 25 Daga Arewa Wani Mukami Mai Muhimmanci

A wani rahoton daban Kungiyar Kare Hakkin Musulmi a Najeriya (MURIC) ta yabi Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf bisa haramta amfani da wasu littattafai a makarantun Nursery da firamare a jihar.

Hassan Indabawa, shugaban kungiyar na reshen jihar Kano ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a 6 ga watan Oktoban 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164