“Lokacin Matasa Ne”: Tinubu Ya Bai Wa Matashiya Yar Shekaru 25 Mukami
- An rahoto cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada matashiya yar arewa a matsayin daya daga cikin hadimansa
- Legit Hausa ta fahimci cewa ana sanya ran wannan matashiya ta taimakawa shugaban kasar wajen cimma ajandarsa ta 'Renewed Hope'
- Koda dai jam'iyyar APC reshen UK ce ta yi karin hanske, fadar shugaban kasa bata rigada ta fitar da jawabi kan haka a hukumance ba
FCT, Abuja - Rahotanni sun kawo cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Ms Fatima Faruk a matsayin babban mai ba shi shawara kan harkokin mata.
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC), reshen Birtaniya ce ta wallafa hakan a shafinta na X.
Tinubu ya bai wa Fatima Faruk mukami
Wallafar da Jam'iyyar APC reshen Birtaniya ta yi a ranar Litinin, 16 ga watan Oktoba na cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Muna taya ki murna Ms Fatima Faruk (mai shekaru 25) kan nada ki a matsayin babbar mai ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu CCFR shawara kan harkokin mata. Lokacin matasa ne."
Tinubu Ya Nada ’Yar Takarar Sanata a Abuja, Adedayo Sakatariyar Hukumar FCTA
A gefe guda, Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Adedayo Benjamins-Laniyi sakatariyar harkokin mata a hukumar Gudanarwa a Abuja (FCTA).
Hukumar ta FCTA ita ta bayyana nadin Adedayo a cikin wata sanarwa a ranar Litinin 16 ga watan Oktoba a Abuja, Legit ta tattaro.
Har ila yau, Adedayo ta yi takarar sanata a jam’iyyar APC a mazabar birnin Abuja a zaben da aka gudanar a wannan shekara ta 2023.
Sanarwar nadin, an yada ta ne a shafin hukumar FCTA na Twitter kamar haka:
“Mai girma Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Adedayo Benjamins-Laniyi a matsayin sakatariyar harkokin mata a hukumar FCTA.”
Uba Sani ya nada sabon SSG a ranar da tsohon sakatare ya zama ministan Najeriya
A wani labarin, Legit Hausa ta rahoto cewa Abdulkadir Muazu Mayere shi ne wanda Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya zaba domin ya zama sakataren gwamnati.
A yammacin ranar Litinin, jawabi ya fito daga ofishin babban sakataren yada labaran Gwamna Uba Sani game da nadin sabon SSG.
Kamar yadda sanarwar ta tabbatar, Muhammad Lawal Shehu ya ce sakataren gwamnatin zai kama aiki ba tare da bata lokaci ba.
Asali: Legit.ng