Uba Sani Ya Nada Sabon SSG a Ranar da Tsohon Sakatare Ya Zama Ministan Najeriya
- Bayan jira na wasu ‘yan kwanaki, Abdulkadir Muazu Mayere ne wanda aka sanar a matsayin sabon Sakataren gwamnatin jihar Kaduna
- Gwamna Uba Sani ya fitar da sanarwa ta musamman ta ofishin Sakataren yada labarai, Mal. Muhammad Lawal Shehu a ranar Litinin
- Dr. Mayere ya yi aiki na sama da shekaru 30 a gwamnatin tarayya, bayan ya yi ritaya ya kama aiki da FOA a majalisar dinkin duniya
Kaduna - Abdulkadir Muazu Mayere shi ne wanda Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya zaba domin ya zama sakataren gwamnati.
A yammacin ranar Litinin, jawabi ya fito daga ofishin babban sakataren yada labaran Gwamna Uba Sani game da nadin sabon SSG.
Kamar yadda sanarwar ta tabbatar, Muhammad Lawal Shehu ya ce sakataren gwamnatin zai kama aiki ba tare da bata lokaci ba.
Uba Sani ya nada Dr. Abdulkadir Mayere
Sanarwar ta ce Dr. Abdulkadir Muazu Mayere ya maye gurbin Mallam Balarabe Abbas Lawal wanda aka rantsar a kujerar Minista.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tribune ta ce kafin yanzu, Abdulkadir Muazu Mayere ya rike kujerar Babban Sakatare a ma’aikatu dabam-dabam na gwamnatin tarayya.
Sabon SSG din ya taba zama Sakataren din-din-din a ma’ikatar karafuna da aikin gona.
Likita ya zama SSG a Kaduna
Abdulkadir Mayere ya shafe shekaru 32 ya na aikin gwamnati a Najeriya, ya fara ne daga likita har ya zama Darekta a shekarar 2011.
Bayan rike Darekta a ma’aikatar wasanni da matasa, sai aka nada shi a matsayin Babban Sakatare a 2017, daga baya sai ya yi ritaya.
Lawal Shehu yake cewa yanzu Dr. Mayere ya na aiki da hukumar abinci ta Duniya watau FAO da ke karkashin Majalisar dinkin duniya.
Gwamna Uba Sani ya yi fatan alheri
"Gwamna Uba Sani ya na sa ran sabon SSG din ya zo da dinbin kwarewarsa wajen cin ma manufofin gwamnati mai-ci.
Ya yi wa Dr. Mayere fatan samun jagoranci da kariyar Allah (SWT) a wannan sabon aikin."
- Muhammad Lawal Shehu
Nada sababbin Ministoci
Tun a safiyar jiya ku ka samu labari Majalisar FEC mai alhakin zartarwa za tayi zama a karkashin jagorancin Mai girma shugaba Bola Tinubu.
A makon nan Dr. Jamila Bio, Ayodele Olawande da Balarabe Abbas Lawal su ka shiga ofis a matsayin ministocin harkar matasa da na muhalli.
Asali: Legit.ng