Akpabio: Shugaban Majalisar Dattawa Ya Musanta Hannu a Tsige Sanata Abbo

Akpabio: Shugaban Majalisar Dattawa Ya Musanta Hannu a Tsige Sanata Abbo

  • Sanata Godswill Akpabi ya musanta zargin da aka masa cewa shi ya yi kutun Kotun Kotu ta tsige Sanata Elisha Abbo
  • Hadimin shugaban majalisar dattawan ya ce babu dalilin da zai sa mai gidansa ya shirya wa abokin aikinsa bi ta da ƙulli
  • Abbo ya yi zargin cewa Akpabio ne ya kulla yadda za a tsige shi da wasu huɗu saboda kawai sun yaƙi shi a zaben majalisa ta 10

FCT Abuja - Shugaban majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya musanta zargin cew da hannunsa Kotun ɗaukaka ƙara ta tsie, Sanata Elisa Abbo, na jam'iyyar APC daga Adamawa.

Idan baku manta ba Kotun ɗaukaka kara ta kori Sanata Abbo, mai wakiltar Adamawa ta arewa, daga majalisar dattawa ranar Litinin, 16 ga watan Oktoba, 2023.

Elisha Abbo da shugaban majalisar dattawa.
Akpabio: Shugaban Majalisar Dattawa Ya Musanta Hannu a Tsige Sanata Abbo Hoto: Elisha Abbo, Godswill Akpabio
Asali: Facebook

Abbo na neman wanda zai ɗora wa laifi ne - Kakakin Akpabio

Kara karanta wannan

Rigima Na Neman Ɓalle Wa a Majalisar Dattawa Yayin da Sanata Ndume Ya Fice a Fusace, Bayanai Sun Fito

Eseme Eyiboh, mai taimaka wa shugaban majalisar dattawa kan harkokin yada labarai ya ce shugabansa ba shi da hannu a hukuncin da kotu ta kori Abbo daga zauren majalisar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Mista Eyiboh na cewa:

"Abin takaici ne idan da gaske ya ce Akpabio ne ya sa hannj aka tsige shi. Wato waƙar swan, wanda wani mutumi ke neman wanza zai ɗora wa laifi."
"Kotun ɗaukaka ƙara da ko wane wuri a faɗin ƙasar nan suna yanke hukunci bisa tanade-tanaden kundin dokokin zaɓe da kuma kwararan hujjojin da masu ƙara suka gabatar."
"Babu wani dalilin da zai sa shugaban majalisar dattawa ya ƙullaci wani abokin aikinsa har ya yi masa zagon ƙasa."

Kotu ta kwace kujerar Sanata Abbo ta bai wa PDP

Idan baku manta ba, Legit Hausa ta kawo muku rahoton yadda Kotun ɗaukaka kara mai zama a Abuja ta rushe nasarar Abbo na APC, ta bai wa ɗan takarar PDP nasara.

Kara karanta wannan

Gwammatin Tinubu Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Mutane Aikin N-Power Na 2023? Gaskiya Ta Bayyana

Sanatan da kansa ya tabbatar da cewa Kotu ta tsige shi, ta ayyana ɗan takarar PDP, Amos Yohanna a matsayin sahihin wanda ya ci zaɓen 25 ga watan Fabrairu.

Amma Sanata Abbo ya tuhumi Akpabio da hannu a kulla makircin da ya jawo Kotun ɗaukaka kara ta yanke wannan hukunci.

Ya kuma ambaci sunan Sanata Orji Kalu , mataayin sanata na gaba da Akpabio ke shirin raba wa da majalisar dattawa ta hanyar hukuncin Kotu, Channels tv ta rawaito.

Shugaba Tinubu Na Shirin Gabatar da Naira Tiriliyan 26 a Matsayin Kasafin 2024

A wani rahoton na daban kuma Gwamnatin Bola Tinubu na shirin gabatar da jimullar Naira tiriliyan 26 a matsayin kasafin kuɗin shekarar 2024.

Ministan kasafin kudi da tsare-tsaren ƙasa, Atiku Bagudu, ne ya bayyana haka ga 'yan jarida a Abuja bayan taron FEC ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262