Akpabio Ne Ya Yi Kutun-Kutun Kotu Ta Tsige Ni Daga Majalisa, In Ji Abbo
- Sanata Elisha Abbo ya zargi shugaban majalisar Dattawa da hannu a kulla makircin tsige shi daga kujerar majalisa
- A dazu ne Kotun daukaka ƙara ta kwace kujerar Abbo, ta bai wa ɗan takarar PDP a zaben Sanatan Adamawa ta arewa
- Da yake martani, Abbo ya ce Akpabio na harin akalla Sanatoci huɗu saboda sun yaƙi kudirinsa na zama shugaban majalisa
FCT Abuja - Sanatan Adamawa ta Arewa da aka tsige, Elisha Abbo, ya zargi shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da hannu a hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke wanda ya cire shi daga ofis.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Kotun daukaka kara da ke Abuja ta rushe nasarar Sanata Abbo na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben 2023.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Abbo a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan Adamawa ta Arewa wan da aka gudanar a ranar 25 ga Fabrairu, 2023.
Yadda sha'ar ta faro tun daga Kotun zaɓe
Amma babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Amos Yohanna, ya yi fatali da sakamakon zaɓen kana ya garzaya Kotu ya shigar da ƙara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun sauraron kararrakin zabe, yayin da ta yanke hukunci, ta yi watsi da karar Yohanna saboda rashin cancanta.
Dan takarar na PDP, ta hannun lauyansa Johnson Usman (SAN), ya wuce gaba zuwa kotun daukaka kara, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Bayan sauraron kowane ɓangare, Kotun ɗaukaka ƙara ta gamsu da bayanan Usman cewa duba da sashi 137 na kundin zaɓe 2022, ya nuna karara cewa sakamakon ya saɓa wa doka.
Daga nan ne kotun ta zabatare kuri’un da basu inganta ba daga jam’iyyu inda ta gano cewa Yohanna na PDP ne ya lashe zaben da mafi rinjayen kuri’u masu inganci.
Akpabio na harin korar wasu Sanatoci daga majalisa
Da yake maida martani kan hukuncin, Sanata Abbo ya ce akwai Sanatoci huɗu da suka yaƙi Akpabio lokacin da yake neman shugabancin majalisar dattawa da ake harin raba su da kujerunsu.
Da yake hira da yan jarida a Abuja, Sanata Abbo ya kira sunan Sanata na gaba da Akpabio ke hari, inda ya ambaci sunan Sanata Orji Uzor Kalu (Abia, APC).
A kalamansa ya ce:
“Na samu labari daga majiya mai tushe cewa ni da wasu Sanatoci hudu a cikin jam’iyyar APC za a cire mu daga majalisar dattawa ta hanyar hukuncim kotu."
"Duk saboda mun yaƙi kudirin zaman Akpabio shugaban majalisar dattawa ta 10. Ba zan ambaci sunayen sauran huɗun ba amma Sanata na gaba a layi shi ne Orji Uzor Kalu."
Shugaba Tinubu Ya Canza Ranar Taron Majalisar Zartarwa FEC Na Mako-Mako
A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya karkashin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya canza ranar gudanar da taron majalisar zartarwa FEC.
Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya ce FG ta amince da maida taron ranar Litinin daga ranar Laraba kuma ba a ko da yaushe ba.
Asali: Legit.ng