Tinubu Ya Yi Barazanar Maka Majalisar Dinkin Duniya Kara a Kotu, Ya Bada Dalili
- Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi barazanar yin karar Majalisar Dinkin Duniya kan zargin almubazaranci da kudi
- Ministan Harkokin Mata ta Tinubu, Uju Kennedy-Ohanenye, ya ce yan Najeriya na bukatar sanin yadda UN ta kashe kudaden da ta karba da sunan Najeriya daga masu bada gudunmawa
- Ta yi barazanar cewa idan UN ta gaza yin bayanin dalla-dalla yadda ta kashe kudin daga yanzu zuwa 15 ga watan Nuwamba ko ta nemi afuwar yan Najeriya, haduwarsu na gaba zai kasance a kotu ne
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta Shugaba Bola Tinubu ta yi barazanar yin karar Majalisar Dinkin Duniya, UN, kan zargin almubarazanci da kudade.
Uju Kennedy-Ohanenye, Ministan Harkokin Mata ce ta yi wannan zargin yayin taron manema labarai a Abuja a ranar Litinin 16 ga watan Oktoba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan na Tinubu ta yi ikirarin cewa Majalisar Dinkin Duniya na karbar kudade a madadin Najeriya daga masa bada gudunmawa kuma ta bukaci dukkan rassan UN su yi wa gwamnati bayanin yadda suka kashe kudaden da suka samu.
Abin da yasa gwamnati ke barazanar karar Majalsar Dinkin Duniya
Ta jadada cewa ya kamata yan Najeriya su ga asusun bankunan kuma su san yadda aka kashe kudaden, ko kuma UN ta nemi afuwar yan Najeriya idan ba za ta iya nuna musu asusun bankunan ba.
Ohanenya ta ce:
"Muna son mu ga abin da suka yi. Idan ba za su iya fada mana ba, a kalla yan Najeriya su ga abin da ke faruwa, idan ba haka ba ku (UN) ku nemi afuwarsu."
Ta yi barazanar cewa:
"Idan ba mu samu rahoton ba daga yanzu zuwa ranar 15 ga watan Nuwamba, za mu tafi kotu."
Ombugadu Na PDP Ya Yi Martani Kan Batun Cewa Zai Tube Rawanin Sarakuna Da Zarar Ya Hau Mulki a Nasarawa
Ta sha alwashin cewa yan Najeriya za su ji sunan lambar karar da aka shigar kuma UN za ta kare kanta dangane da kudaden da ta karba da sunan yan Najeriya.
UN da rassanta sun kasance suna yin ayyukan jin kai a Najeriya, musamman a bangarorin lafiya, mata da cigaba da yara da shirye-shiryen rage talauci.
Ga bidiyon taron manema labaran a kasa:
Asali: Legit.ng