Jam'iyyar APC Ta Dage Yakin Neman Zaben Gwamana a Jihar Bayelsa
- Jam'iyyar APC ta ɗage gangamin kaddamar da yaƙin neman zaɓen ɗan takararta na gwamna a zaben Baylesa
- Kakakin APC, Felix Morka, ya ce an ɗage kaddamar da kamfen daga ranar Asabar, za a sanar da sabuwar rana nan gaba
- Wannan mataki na zuwa ne bayan babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja ta hana tsohon ministan mai, Sylva, takara
FCT Abuja - Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta dage kaddamar da yakin neman zaben gwamnan jihar Bayelsa da aka shirya yi a ranar Asabar ɗin nan.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanya ranar 11 ga watan Nuwamba domin gudanar da zaben gwamnoni a jihohin Bayelsa, Kogi da kuma Imo.
Jam’iyyar APC, wadda ta kaddamar da kamfen dinta a jihohin Kogi da Imo, ta zaɓi ranar Asabar, 14 ga watan Oktoba, 2023 domin buɗe fagen yakin neman zabenta a jihar Bayelsa.
Amma mai magana da yawun APC ta ƙasa, Felix Morka, ya ce an ɗaga kaddamar da kamfen zaben gwamnan Bayelsa a wata sanarwa da ya sa wa hannu ranar Jumu'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwan wadda aka wallafa a shafin APC na manhajar X watau Twitter, ta ce za a sanar da sabuwar ranar buɗe fagen kamfe ɗin idan jam'iyyar ta cimma matsaya.
Sanarwan ta yi bayanin cewa:
"Jam'iyyar APC na sanar da dage kaddamar da yakin neman zaben gwamnan jihar Bayelsa da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar 14 ga Oktoba, 2023 a Yenagoa, babban birnin jihar."
"Za a sanar da sabuwar ranar gangamin buɗe fagen kamfe a lokacin da ya dace da zaran an sanya sabon lokaci."
Meyasa jam'iyyar APC ta ɗage kamfen Bayelsa?
A halin da ake ciki, jam'iyyar APC ba ta bayyana ainihin dalilin da ya haddasa ta ɗage yaƙin neman zaɓe a Bayelsa ba.
Amma ana hasashen cewa ba zai rasa nasaba da soke takarar Timipre Sylva, ɗan takarar gwamna a inuwar APC, wanda babbar Kotun tarayya ta yi.
Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban FERMA da Majalisar Gudanarwa
Kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya rushe majalisar gudanarwa ta hukumar kula da kyaun titunan gwamnatin tarayya FERMA.
Shugaban ya kuma amince da naɗa sabbin waɗanda zasu jagoranci hukumar na tsawon shekara huɗu masu zuwa.
Asali: Legit.ng