Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban FERMA da Majalisar Gudanarwa
- Bola Ahmed Tinubu ya rushe majalisar gudanarwa ta hukumar kula da kyaun titunan gwamnatin tarayya FERMA
- Shugaban ya kuma amince da naɗa sabbin waɗanda zasu jagoranci hukumar na tsawon shekara huɗu masu zuwa
- Tinubu ya buƙaci waɗanda aka naɗa su maida hankali wajen hidimtawa al'umma duba da muhimmancin aikin FERMA
FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rusa tsohuwar majalisar gudanarwa ta hukumar kula da tituna ta tarayya (FERMA), kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Chief Ajuri Ngelale, shi ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a, 13 ga watan Oktoba, 2023.
Ya ce shugaban ƙasan ya nada sabuwar tawaga na tsawon shekaru hudu (4), wanda ya yi daidai da sashe na 2 (3) na kundin dokokin FERMA, 2007 da aka yi wa kwaskwarima.
Sanarwan ta ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Shugaba Tinubu na fatan sabbin wadanda aka nada za su maida hankali wajen hidimta wa ƙasa, idan aka yi la’akari da muhimmiyar rawar da hukumar ke taka wa wajen lafiyar tituna faɗin Najeriya."
Jerin sunayen sabbin mutanen da Tinubu ya naɗa a FERMA
1. Shugaban Hukumar FERMA - Injiniya Imam Ibrahim Kashim Imam
2. Manajan Darakta na hukumar FERMA - Injiniya Chukwuemeka Agbasi
3. Mamba (NARTO) - Yusuf Lawal Othman
4. Mamba (FMW) - Injiniya Ibi Terna Manasseh
5. Mamba (FRSC) - ACM Shehu Mohammed
6. Mamba (sashin kuɗi) - Babatunde Daramola-Oniru
7. Mamba (Kudu maso Kudu) - Hon. Preye Oseke
8. Mamba (Kudu maso Yamma) - Hon. Oye Ojobe
9. Mamba (Kudu maso Gabas) - Dakta Kenneth Ugbala
10. Mamba (Arewa ta Tsakiya) - Sanata Timothy Adudu
11. Mamba (Arewa maso Gabas) - Injiniya Abubakar Bappa
12. Mamba (Arewa maso Yamma) - Aminu Adamu Papa.
Daga ƙarshe, Shugaban ƙasa ya yi musu fatan Alheri da kuma fatan zasu yi aiki tuƙuru duba da muhimmancin aikin FERMA, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
Shugaba Tinubu Ya Ɗauko Kakakin PCC da Wata Mace, Ya Naɗa Su a Muhimman Muƙamai
A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Bayo Onanuga, tsohon mai magana yawun PCC-APC a matsayin mai bada shawara ta musamman.
Ya kuma naɗa Mis Delu Bulus Yakubu a matsayin babbar mai taimaka masa kan harkokin jin ƙai da yaƙar talauci.
Asali: Legit.ng