Dan Majalisar ADC da Shugaban Jam'iyya Sun Koma APC a Jihar Kogi

Dan Majalisar ADC da Shugaban Jam'iyya Sun Koma APC a Jihar Kogi

  • Shugaban ADC a jihar Kogi da dumbin mambobi sun ayyana goyon baya ga ɗan takarar gwamna a inuwar APC, Usman Ododo
  • Haka nan kuma ɗan majalisar ADC, Idowu Ibikunle, ya ce duk da a inuwar jam'iyyar ya ci zaɓe amma ɗan takarar APC yake so a zaɓen gwamna
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake tunkarar zaben gwamnan jihar Kogi ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023

Jihar Kogi - Shugaban tsagi ɗaya na jam'iyyar African Democratic Party (ADC) reshen jihar Kogi, Kingsley Oga, da wasu jiga-jigan mambobi sun koma bayan APC.

Rahoton Vanguard ya tattaro cewa tawagar jiga-jigan yan siyasar daga mazaɓun Sanatocin jihar guda uku sun yi watsi da ɗan takarar gwamna a inuwar ADC, Leke Abejide.

Jiga-Jigan ADC sun mara wa APC baya a Kogi.
Dan Majalisar ADC da Shugaban Jam'iyya Sun Koma APC a Jihar Kogi Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Sun kuma ayyana goyon bayansu ga mai neman zama gwamna karkashin jam'iyyar APC, Usman Ododo, a zaɓen gwamna mai zuwa a watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 6 Na Arewa Sun Gana a Katsina, Sun Cimma Matsaya Kan Muhimman Abu 2

Mista Ogah ne ya bayyana haka yayin da su ke tabbatar da mubaya'arsu ga ɗan takarar APC a gidan gwamnatin Yahaya Bello da ke Lokoja ranar Jumu'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce yana nan daram a matsayin shugaban ADC na jiha, amma sun yanke shawarar watsi da dan takarar jam’iyyar, su yi wa dan takarar APC aiki.

A jawabinsa, Ogah ya ce:

"A cikin dukkan ’yan takarar gwamna a zabe mai zuwa ranar 11 ga watan Nuwamba, dan takarar APC, Alhaji Ododo Usman ne ya fi cancanta."
“Kafin yau na kafa kwamitin mutum biyar domin tantance duk ‘yan takarar da suka nuna sha'awa. A karshe rahoton kwamitin ya nuna cewa Alhaji Ododo Usman ne ya dace mu danƙa wa amana."

Abin da ya sa muka juya wa ADC baya

Mista Ogah ya ƙara cewa namijin kokarin da gwamna Yahaya Bello ya yi wajen kawo ci gaba a jihar Kogi, yana buƙatar a samu wani ɗan halak da zai ɗora daga nan.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Samu Koma Baya, Manyan Jiga-Jiganta Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar APC

Ya ce saboda haka ne dukkansu suka yanke shawarar marawa Alhaji Usman baya a zabe mai zuwa, Tribune ta rawaito.

Ya yabawa Gwamna Bello bisa nasarorin da ya samu a fadin jihar cikin shekaru bakwai da rabi na gwamnatinsa.

Ɗan majalisar ADC ya marawa Ododo baya

A nasa jawabin, Idowu Ibikunle, mai wakiltar Yagba ta Yamma a majalisar dokokin Kogi, ya ce duk da cewa ya ci zaɓe a inuwar ADC, shi da magoya bayansa suna tare da Ododo na APC.

"Gwamna Yahaya Bello ya taka rawar gani kuma saboda haka zan marawa dan takararsa baya. Muna fatan gwamna mai jiran gado, Ododo, ya ɗora daga nan a 2024."

Mun Daina Adawa da Tikitin Musulmi da Musulmi, Shugabannin Kiristoci

A wani rahoton kuma Kiristocin Najeriya sun canza tunani kan adawar da suka yi da tikitin Musulmi da Musulmi na Tinubu da Shettima a zaben 2023.

Kara karanta wannan

A Karo Na Biyu, Gwamnan PDP Ya Ɗauko Ɗan Takarar Jam'iyyar Adawa, Ya Naɗa Shi a Muƙami Mai Gwaɓi

A cewarsu, shugaba Tinubu da Shettima sun kwatanta adalci da daidaito a naɗe-naɗen da suka yi kawo yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262